Mazauna garin Taraba da yan awaren Kamaru suka kashe basarake sun yi kaura

Mazauna garin Taraba da yan awaren Kamaru suka kashe basarake sun yi kaura

  • Mazauna wasu garuruwa a karamar hukumar Takum ta jihar Taraba sun tsere sun bar yankin bayan da yan awaren Kamaru suka kai masu farmaki
  • A ranar Laraba,17 ga watan Nuwamba ne yan awaren na Ambazonia suka kai farmaki garuruwan iyakar inda suka kashe wani Basarake da wasu 11
  • Shugaban karamar hukumar ya ce sun gano gawarwaki biyar sannan har yanzu ba a ga wasu ba

Taraba - Daruruwan mazauna garuruwan da ke iyakar Taraba sun tsere daga gidajensu biyo bayan kisan mutane 11, ciki harda wani basarake da yan awaren kasar Kamaru suka yi, rahoton Daily Trust.

Yan awaren na Ambazonia sun kai farmaki wasu garuruwa da ke kan iyaka a karamar hukumar Takum a ranar Laraba, 17 ga watan Nuwamba sannan suka kashe mutum 11.

Read also

Sabon farmakin da 'yan fashin daji suka kai Sokoto ya lamushe rayuka 14

Mazauna garin Taraba da yan awaren Kamaru suka kashe basarake sun yi kaura
Mazauna garin Taraba da yan awaren Kamaru suka kashe basarake sun yi kaura Hoto: Channelstv.com
Source: Twitter

Mayakan sun kuma kona gidaje da makarantu da dama sannan suka yi awon gaba da kayayyaki.

Shugaban karamar hukumar Takum, Mista Shiban Tikari, ya ce an gano gawarwakin mutane biyar da aka kashe sannan har yanzu ba a ga wasu da dama ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya kuma kawo cewa Tikari ya ce an zuba sojoji daga Takum domin su kare garuruwan iyakar daga yan aware da sojojin Kamaru da ke ta kai hari garuruwan iyaka a kananan hukumomin Kurmi da Takum da ke jihar.

A watan da ya gabata, an tattaro cewa sojojin Kamaru sun fatattaki garuruwan iyaka uku a karamar hukumar Kurmi da ke jihar bayan sun fake da neman yan awaren Ambazonia.

'Yan aware daga Kamaru sun shigo Najeriya, sun kashe mutane, sun kone gidaje

A baya mun kawo cewa, wasu da ake zargin 'yan awaren Ambazonia ne daga kasar Kamaru sun yi barna a karamar hukumar Takum da ke jihar Taraba.

Read also

'Yan aware daga Kamaru sun shigo Najeriya, sun kashe mutane, sun kone gidaje

A cewar mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Emmanuel Bwacha, wadanda ake zargin sun bindige hakimin kauye da wasu mazauna unguwar Manga.

Kauyen Manga yana da tazarar kilomita 20 daga Dam din Kashimbilla.

Source: Legit.ng

Online view pixel