Sabon farmakin da 'yan fashin daji suka kai Sokoto ya lamushe rayuka 14

Sabon farmakin da 'yan fashin daji suka kai Sokoto ya lamushe rayuka 14

  • An halaka a kalla mutane 14 sakamakon farmakin da ‘yan bindiga suka kai garuruwan da ke karkashin karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto
  • Sun kai farmaki garin ne bayan sa’o’i kadan da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kara tura wasu sojoji yankin don kawo garanbawul akan matsalar tsaro
  • Mazauna Sabon Birni sun bayyana yadda ‘yan bindigan suka fada wasu kauyuka da ke karkashin Unguwan Lalle a ranar Talata da dare

Sokoto - A kalla mutane 14 ne su ka rasa rayukansu yayin da ‘yan bindiga suka kai farmaki wasu garuruwa da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

An kai farmakin ne bayan sa’o’i kadan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara tura wasu sojoji zuwa jihar don kawo gyara akan matsalar tsaro, Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun sheke maharbi, sun tasa keyar mutum 30 a Niger

Sabon farmakin da 'yan fashin daji suka kai Sokoto ya lamushe rayuka 14
Sabon farmakin da 'yan fashin daji suka kai Sokoto ya lamushe rayuka 14. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Wani mazaunin Sabon Birni, wanda ya tabbatar da farmakin ya ce ‘yan bindigan sun afka wasu kauyuka da ke Unguwan Lalle, a ranar Talata da dare.

A cewarsa, sun halaka wani Abdullahi Usman a Unguwan Lalle, sannan sun halaka mutane 9 a kauyen Tsangerawa da wasu 4 a Tamindawa.

Sun bude wa wata motar haya wuta a kauyen Gajid wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 3, ciki har da direban.

Sauran fasinjoji 5 duk sun samu raunuka kuma yanzu haka su na asibiti ana kula da su.

‘Yan bindigan sun yi garkuwa da wasu mutane 3 a kauyen. Daga baya an sake su bayan yarjejeniyar za a biya N2,000,000 cikin wasu kwanaki.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Kamaluddeen Okunlola ya ce ‘yan bindigan sun halaka mutane 8 sakamakon farmakin.

Kara karanta wannan

Da duminsa: ISWAP sun sake kai hari, suna luguden wuta a Borno da kone gidaje

A wata tattaunawa da kwamishinan ya yi da Daily Trust, ya ce:

“Sun kai farmaki wasu kauyuka duk da babu hanyoyi masu kyau. Da yardar Ubangiji sai mun kama su kuma muna aiki akansu.
“Ko jiya da dare sai da Shugaban Kasa ya turo wasu sojojin zuwa Sokoto,”

ISWAP sun tilasta wa manoman kauyukan Borno biyan haraji, sun ce zakkar gona ce

A wani labari na daban, jama'a masu zama wasu daga cikin kauyukan Borno sun koka da halin da suka samu kansu na tilascin biyan haraji da 'yan ta'adda suka saka musu a cikin zakkar amfanin gona.

Kamar yadda BBC ta wallafa, jama'a mazauna garin Damboa sun sanar da yadda 'yan ta'addan ke amfani da karfi wurin kwace amfanin gona da dabbobi, kuma biyayya a gare su ta zama dole domin tsira.

Wannan al'amarin ya kara fitowa ne a lokacin da ake cigaba da rade-radin cewa 'yan ta'addan ISWAP na amshe haraji daga wurin makiyaya da manoman jihar Borno.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bayan harin Islamiyya, Tsagerun yan bindiga sun sake mamaye Tegina, sun sace ma'aikata

Asali: Legit.ng

Online view pixel