An damƙe sojan bogi yayin da ya tafi karɓo abokinsa a hannun 'yan sanda da bindigar katako

An damƙe sojan bogi yayin da ya tafi karɓo abokinsa a hannun 'yan sanda da bindigar katako

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta kama wani da ake zargin sojan bogi ne yayin da ya ke kokarin amsar abokinsa daga hannunsu
  • Kakakin rundunar, Wasiu Abiodun ya ce sun kama mai laifin, Emmanuel Dominic a wuraren Tunga a Minna ranar 27 ga watan Oktoba
  • Ya isa ofishin ‘yan sandan sanye da kayan sojoji ne, inda ya gabatar da kansa a matsayin soja, da tambayoyi su ka yi nisa aka gane ba sojan gaske bane

Jihar Neja - Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta kama wani sojan gona yayin da ya ke kokarin amsar abokinsa daga hannunsu.

Wasiu Abiodun, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ya ce an kama mai laifin ne, Emmanuel Dominic a kusa da unguwar Tunga da ke Minna ranar 27 ga watan Oktoba, The Cable ta ruwaito.

Read also

Da duminsa: 'Yan bindiga sun sheke maharbi, sun tasa keyar mutum 30 a Niger

An damke sojan bogi yayin da ya tafi karbo abokinsa a hannun 'yan sanda da bindigar katako
An kama sojan bogi yayin da ya tafi karbo abokinsa a hannun 'yan sanda da bindigar katako. Hoto: The Cable
Source: Facebook

Kakakin yan sandan ya bayyana cewa:

“Wanda ake zargin ya sa kayan sojojin Najeriya sannan ya nufi har ofishin ‘yan sandan tare da gabatar da kansa a matsayin soja mai lamba 05313 na TRADOC a Minna, inda ya bukaci a saki abokinsa da ke hannun ‘yan sandan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Bayan shan tambayoyi, an gano ashe sojan gona ne sannan aka kama shi.
“Abubuwan da aka samu a hannunsa sun hada da bindigar toka, adduna 2, wuka 1, jakunkuna 2, korayen wanduna 2, rigar sojoji, hula da kuma sanda.”

Kakakin ya ce wanda ake zargin ya dade yana fashi a Minna da kewaye

Abiodun ya kara da cewa wanda ake zargin ya dade ya na fashi a Minna da kewaye da bindigar tokarsa, adda da wuka.

Har ila yau, kakakin ya kara da bayyana yadda su ka samu nasarar kama wasu matasa da ke lalata na’urar kara wutar lantarki a ranar 7 ga watan Nuwamba.

Read also

Asirin kuɗi: An kama wani mutum da ya haɗa baki da malamin addini mai shekaru 95 don kashe ɗan cikinsa

Ya bayyana sunayensu inda ya ce akwai Hussaini Adamu, Mustapha Umar, Mande Magaji, Suleiman Zubairu da Salisu Usman.

A cewar Abiodun, an kama wadanda ake zargin ne a wurin na’urar, sai kuma Salisu Usman a Kasuwan-Gwari wanda ‘yan sanda su ka tasa wa keya don ya dauko musu wayoyin wuta.

'Yan sanda sun yi ram da wasu samari 2 bayan sun datse wa juna hannaye yayin kwasar dambe

A wani labarin, 'yan sanda sun yi ram da samari 2 bisa kama su dumu-dumu da laifin sare wa juna hannaye, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

An ruwaito yadda ‘yan sandan su ka kama Adamu Mohammed da Bukar Audu, bayan sun datse wa juna hannaye yayin wani fada da su ka tafka a Garin Alkali, karamar hukumar Dapchi da ke jihar Yobe.

Premium Times ta bayyana yadda Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, a ranar Litinin a Damaturu ya bayyana a wata takarda.

Source: Legit.ng

Online view pixel