Daga Obasanjo zuwa Buhari: Jerin basusukan da shugabannin Nigeria 4 suka karɓo daga 1999 zuwa 2021

Daga Obasanjo zuwa Buhari: Jerin basusukan da shugabannin Nigeria 4 suka karɓo daga 1999 zuwa 2021

  • Kwanan nan aka yi ca akan Muhammadu Buhari lokacin da ya bayyana bukatar amso basuka gaban majalisar tarayya
  • Shugaban kasan Najeriyan ya bukaci majalisar ta amince a aro $4,054,476,863.00, €710m da kuma $125m daga kasashen ketare
  • ‘Yan Najeriya da dama sun dinga cece-kuce akan irin yawan basukan da gwamnatin nan ta ke amsowa duk don ginin kayan masurufi duk da halin da kasa take ciki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya janyo cece-kuce inda ‘yan Najeriya da dama su ka dinga suka lokacin da ya bukaci Majalisar Dattawa ta amince da bukatarsa ta amso bashi.

Shugaban kasar Najeriya ya bukaci Majalisar Tarayya ta amince a karbo bashin $4,054,476,863.00, €10m da kuma $125m.

Daga Obasanjo zuwa Buhari: Jerin basusukan da shugabannin Nigeria 4 suka karɓo
Daga Obasanjo zuwa Buhari: Jerin basusukan da shugabannin Nigeria 4 suka ciwo. Photo credit: Femi Adesina, Goodluck Jonathan, BBC Hausa
Asali: Facebook

‘Yan Najeriya da dama sun nuna rashin amincewarsu da amsar bashin don inganta kayan more rayuwa duk da halin da kasa take ciki.

Kara karanta wannan

Yadda Buhari ya tattaro biliyoyin da aka sace, aka boye a Amurka, Ingila da Switzerland

Basukan da ake bin Najeriya su na ta kara hauhawa. A watan Maris din 2021, ana bin Najeriya bashin naira tiriliyan 33.1 ($87.24b); bashin da aka tattara har da na gwamnatin da ta gabata.

Kwanan nan The Cable ta ruwaito yadda duk da yadda gwamnatin Olusegun Obasanjo ta jajirce wurin dakata ci gaba da aro kudade, gwamnatin da ta gaje ta ta ci gaba da cin bashin.

Jaridar ta bayyana yadda basukan da ake bin gwamnatin tarayya su ka karu da 658% zuwa Naira tiriliyan 26.9 cikin shekaru 21 da suka gabata.

Bayan tattaro bayanai daga ofishin kula da bashuka (DMO), an samu rahoto akan basuka (Na ciki da wajen kasa) su ka hauhawa daga naira tiriliyan 3.55 a 1999 zuwa naira tiriliyan 26.91 a karshen watan Maris din 2021.

Kara karanta wannan

Yajin aikin ASUU: Kakakin majalisa ya gayyaci ministar kudi, na ilimi da shugaban ASUU

Tun 1999 da Najeriya ta koma dimokradiyya, Najeriya ta yi shugabannin kasa 4, Olusegun Obasanjo, Umaru Yar’Adua, Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari.

Wannan rahoton ya yi dubi ga shugabancin mutane 4.

1. Tsohon shugaba Obasanjo

Bashin kasashen waje: Sun ragu daga $28.04b a 1999 zuwa $2.11b a 2007

Bashin cikin gida: Ya karu daga naira biliyan 789 zuwa naira tiriliyan 2.11

Bashin gwamnatin tarayya: Ya ragu daga Naira tiriliyan 3.55 a 1999 zuwa naira tiriliyan 2.42 a 2007

Bashin gwamnatin tarayya na cikin fida da waje: Ya ragu da 31.8%

Darajar musayar kudi ta ragu: N98.02/ N116.8 zuwa $1

2. Yar’Adua/Jonathan (2007 zuwa 2011)

Bashin kasashen waje - Ya ragu daga $2.11b a 20017 zuwa $3.5b a 2011

Bashin cikin gida: Ya karu daga Naira tiriliyan 2.17 a 2007 zuwa Naira tiriliyan 5.62 a 2011

Darajar kudin musaya: Ya karu daga N116/$1 zuwa N156.7/$1

Kara karanta wannan

Yadda Buhari yake kashe makudan biliyoyi wajen sayen motoci, yana laftowa Najeriya bashi

An samu karuwar 155%

Abin lura

Jonathan ya kammala shekarun sa daga Mayun 2010 zuwa Mayun 2011 bayan mutuwar Yar’Adua.

Lokacin an samu bayanai akan yadda bashin ya hau daga Naira tiriliyan 4.94 zuwa naira tiriliyan 6.17 (karin 24.9% cikin shekara daya).

3. Tsohon Shugaba Goodluck Jonathan

2011:

Basukan Waje: $3.5b

Basukan Cikin Gida: N5.62 tiriliyan

Basukan da ya tattaro Naira tiriliyan 6.17

Basukan kasar waje na 2014: $6.45b

Basukan cikin gida: Naira tirilyan 7.9

Gabadaya basuka daga 2011 zuwa 2015: Sun karu da 58.8%

Shugaba Muhammadu Buhari

2015:

Bashin Kasashen Waje: $7.35b

Bashin Cikin Gida: Naira Tiriliyan 16.02

Bashin Cikin Gida: Ya karu da Naira Tiriliyan 7.63 (daga Yunin 2015 zuwa Disamban 2020)

Basukan Waje: Sun karu da $21.27b (Daga Disamban 2020

Darajar Musayar Kudi: 173.2% daga 2015

The Cable ta ruwaito yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya fi ko wanne shugaba cin bashi inda bashi ya karu da fiye da kaso 173%

Kara karanta wannan

Gumi ya caccaki 'yan aware: Igboho da Kanu ne suka kunna wutar rikicin Fulani a kudu

Gwamnatin ‘Yar’Adua ta zama ta biyu inda bashi ya karu da 155%.

Gwamnatin Jonathan ta zama ta uku inda bashi ya karu da 58.8%. Gwamnatin Obasanjo ce kadai ta rage bashin da ake bin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel