Yadda Buhari ya tattaro biliyoyin da aka sace, aka boye a Amurka, Ingila da Switzerland

Yadda Buhari ya tattaro biliyoyin da aka sace, aka boye a Amurka, Ingila da Switzerland

  • Gwamnatin tarayya tayi bayanin hanyar da ta bi, ta dawo da makudan kudin da aka sace a Najeriya
  • Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN ne ya bayyana wannan a wajen wani taro a kasar Amurka
  • Malami yace shugaba Muhammadu Buhari ya bankado kudin sata a Amurka, Ingila, da kasar Ireland

Abuja - Gwamnatin tarayya tayi karin haske a kan yadda ta dauki matakai domin maganin sata, har tayi nasarar dawo da dukiyar al’umma da aka kai ketare.

Jaridar Punch tace kudin da aka sata daga kasar nan, aka dankare a kasar waje sun hada da Dala miliyan $322.515 da aka boye a bankunan kasar Switzerland.

Akwai Dala miliyan $311.7 da aka gano a Amurka, da fam miliyan €5.4 a kasar Northern Ireland da wasu Dala miliyan $200 da miliyan €4,214,017.66 a Birtaniya.

Kara karanta wannan

Yajin aikin ASUU: Kakakin majalisa ya gayyaci ministar kudi, na ilimi da shugaban ASUU

Babban lauyan gwamnatin tarayya, kuma Ministan sharia’a na kasa, Abubakar Malami ya bayyana wannan a wani jawabi da ya yi ta bakin Dr. Umar Gwandu.

Mai magana da yawun bakin Ministan yace Malami ya yi wannan jawabi ne wajen wani taro da aka shirya a birnin New York, kasar Amurka a ranar Litinin dinnan.

Malami yace shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a matsayinsa na jagoran yaki da rashin gaskiya na Afrika, ya kawo dokokin yaki da satar kudin jama’a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari Hoto: www.aljazeera.com
Asali: UGC

An samu nasarori daga 2017 zuwa yau

“A 2017, aka sa hannu a yarjejeniya da kasar Switzerland da kuma bankin Duniya, da ya bada dama a dawo da wasu Dala miliyan $322.515.”
“A 2020, aka tattara Dala miliyan $311.7 aka dawo da wasu Najeriya, bayan sa hannu a wata yarjejeniya da Amurka da Bailiwick ba Jersey.”

Kara karanta wannan

Manyan gobe: Hazikan matasa 'yan Najeriya 3 da suka kera motocin a zo a gani da kansu

“Har ila yau a 2020, aka dawo da fam miliyan €5.4 a dalilin wata yarjejeniya da aka shiga da kasar Northern Ireland.” – Abubakar Malami SAN.

An gano dukiyar da iyalin James Ibori suka sace

A cewar Ministan shari’an, gwamnatin Buhari ta iya dawo da fam €4,214,017.66 da iyalan James Ibori suka sace daga Najeriya, suka boye a kasar Birtaniya.

Vanguard ta rahoto Malami yana cewa ana jiran kudi har fam miliyan $200 daga kasashen waje.

Shari'ar VAT ta jawo babbar magana

An ji cewa Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki tace za a zauna a wajen kotu kan shari’ar VAT da wasu jihohi suka shigar, su na kalubalantar FIRS.

Zainab Ahmed tana so a hakura da maganar zuwa kotu, a zauna a samu mafita da gwamnoni. Ahmed tana ganin cewa Alkali ba zai iya magance matsalar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel