Muna ciyar da dalibai milyan 9 kulli yaumin a Najeriya, Minista Sadiya Farouq

Muna ciyar da dalibai milyan 9 kulli yaumin a Najeriya, Minista Sadiya Farouq

  • Hajiya Sadiya Umar Farouq ta bayyana adadin daliban da ake ciyarwa kulli yaumin a fadin tarayya
  • Ministar ta ce shirin ya samu karbuwa sosai a jihohin Najeriya kuma jama'a suna amfana sosai da sosai
  • Hajiya Sadiya ta bayyana cewa an tsara shirin ne domin tsomo yan Najeriya daga cikin bakin talauci

Ministar tallafi, walwala da jin dadin al'umma, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa sama da dalibai milyan tara na amfana da shirin ciyar da daliban firamare abinci watau NHGSFP.

Kamfanin dillancin labarai NAN ya ce Ministar ta bayyana hakan ne yayin taron mika kayan girki ga gwamnatin jihar Benue a LGEA Wurukum.

Sadiya, wacce ta samu wakilcin Mataimakin Dirakta Ladan Haruna, ta bayyana cewa an tsara shirin ne domin tsomo yan Najeriya daga cikin bakin talauci.

Kara karanta wannan

Yajin aikin ASUU: Kakakin majalisa ya gayyaci ministar kudi, na ilimi da shugaban ASUU

Ta ce an dauki masu girki sama da 100,000 a fadin tarayya.

Ministar ta baiwa al'ummar Najeriya tabbacin cewa ba za tayi kasa gwuiwa wajen tabbatar da jin dadinsu ba.

Muna ciyar da dalibai milyan 9 kulli yaumin a Najeriya, Minista Sadiya Farouq
Muna ciyar da dalibai milyan 9 kulli yaumin a Najeriya, Minista Sadiya Farouq
Asali: Twitter

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, wanda ya karbi bakuncin kayayyaki yace lallai kayayyakin da kudinsu ya kai N400 million zai taimaka matuka.

Gwamna wanda ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin jihar, Farfesa Tony Ijohor, yace gwamnatinsa ta horar da masu girkin kan tsafta da bin dokokin COVID-19.

Mun kashe Bilyan 2 wajen ciyar da daliban firamare a jihar Adamawa kadai, Hajiya Sadiya

Gwamnatin tarayya ta ce ta kashe akalla bilyan biyu wajen ciyar da daliban makarantun jihar Adamawa kadai karkashin shirin ciyar da dalibai a fadin tarayya.

Kara karanta wannan

EndSARS: Gwamnati ta yi karya, lallai an kashe dimbin matasa a Lekki Toll Gate, Kwamitin binciken jihar Legas

Ministar tallafi da walwala, Hajiya Sadiya Umar Faoruq, ta bayyana hakan ne a taron bada kayan girki 50,000 ga gwamnatin jihar Adamawa ranar Asabar a Yola.

Ta yi bayanin cewa gwamnatin tarayya na kashe ₦226 million a wata don ciyar da dalibai a jihar Adamawa.

Tace kawo yanzu, sama da dalibai milyan 9 aka yiwa rajista kuma sun amfana da wannan shiri a fadin tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel