Mun kashe Bilyan 2 wajen ciyar da daliban firamare a jihar Adamawa kadai, Hajiya Sadiya Farouq

Mun kashe Bilyan 2 wajen ciyar da daliban firamare a jihar Adamawa kadai, Hajiya Sadiya Farouq

  • Hajiya Sadiya Farouq ta bayyana adadin daliban da ake ciyarwa kullum a Adamawa
  • Ministar ta ce shirin ya samu karbuwa sosai a jihar Adamawa
  • Gwamnati ta na kashe kimanin milyan 230 a wata don ciyar da dalibai

Yola - Gwamnatin tarayya ta ce ta kashe akalla bilyan biyu wajen ciyar da daliban makarantun jihar Adamawa kadai karkashin shirin ciyar da dalibai a fadin tarayya.

Ministar tallafi da walwala, Hajiya Sadiya Umar Faoruq, ta bayyana hakan ne a taron bada kayan girki 50,000 ga gwamnatin jihar Adamawa ranar Asabar a Yola, rahoton Tribune.

Sadiya Farouq, wacce ta samu wakilcin Dr. Umar Bindir, jagoran shirin walwala ta kasa, yace shirin ciyar da dalibai na cikin manyan shirye-shirye hudu na ma'aikatar.

Kara karanta wannan

Bidiyon Jami'an yan sanda yayinda suka damke karya kan laifin cizon dalibin jami'a a azzakari

Ta yi bayanin cewa gwamnatin tarayya na kashe ₦226 million a wata don ciyar da dalibai a jihar Adamawa.

Tace kawo yanzu, sama da dalibai milyan 9 aka yiwa rajista kuma sun amfana da wannan shiri a fadin tarayya.

Tace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sama da ₦2 billion gwamnatin tarayya ta kashe a Adamawa, karkashin shirin ciyar da daliban makarantu firamare(NHGSFP)."
"Na zo nan don wakiltan Shugaban kasa, domin mika kayan girki 50,000 ga gwamnatin jihar Adamawa, don amfani da su wajen ciyar dalibai."
"Kawo yanzu, shirin ta yi rijistan dalibai milyan tara da ake ciyarwa kuma an dauki masu girki sama da 100,000."

Mun kashe Bilyan 2 wajen ciyar da daliban firamare a jihar Adamawa kadai, Sadiya Farouq
Mun kashe Bilyan 2 wajen ciyar da daliban firamare a jihar Adamawa kadai, Hajiya Sadiya Farouq Hoto: NHGSFP
Asali: Twitter

Dalibai 162,782 dake ciyarwa a Adamawa kullum

A cewar Ministar, shirin da aka ya samu karbuwa a jihar Adamawa tun da kawo yanzu yana gudana a makarantu 1,286, ana ciyar da dalibai 162,782, kuma an dauki masu girki 2,417.

Kara karanta wannan

Mata mafarauta: A bamu wuka da nama, harsashi ba ya ratsa mu, za mu iya da 'yan bindiga

Ta ce an raba kayan girkin ne domin tabbatar da tsaftar abincin da ake baiwa dalibai.

Survival Fund: Gwamnati ta raba wa 'yan Najeriya sama da miliyan 1 kudade N56.8bn

A bangare guda, Maryam Katagum, karamar ministar masana’antu, kasuwanci da saka hannun jari, ta ce gwamnatin tarayya ta raba naira biliyan 56.8 ga mutane sama da miliyan 1 - ciki har da wadanda aka yi wa rajista a karkashin Hukumar Kula da Harkokin Kamfanoni (CAC).

Ministar, wacce kuma itace shugabar kwamitin kula da shirin Survival Fund, ta fadi hakan ne a wani taron manema labarai a ranar Talata 31 ga watan Agusta a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel