Bayan na ki kwanciya da malamina, ya ce na zane shi, Dalibar da aka kora, ta kammala digiri daga baya

Bayan na ki kwanciya da malamina, ya ce na zane shi, Dalibar da aka kora, ta kammala digiri daga baya

  • Wata budurwa 'yar Najeriya ta yi murnar kammala digirin ta daga jami'ar fasaha ta gwamnatin tarayya da ke Owerri duk da kalubalen da ta fuskanta
  • Mai digirin cike da farin ciki, wacce aka kora amma daga baya aka sake kiran ta, ta ce akwai lakcaran da yayi kokarin kwanciya da ita amma ta ki bada hadin kai
  • Dalibar da ta bayyana cewa a kowacce rana ta na zuwa aji da jinjiri, ta ce malamin daga bisani ya ce ta zane shi bayan duk kokarinsa na kwanciya da ita ya gaza

Wata budurwar Najeriya da ta kammala digirin ta na farko duk da matsalolin da ta fuskanta ta jajirce.

A wata wallafa da Instablog9ja ta wallafa a Instagram, dalibar da ta kammala karatun ta daga jami'ar fasaha ta tarayya da ke Owerri, ta wallafa hoton ta sanye da riga an rubuta "an kore ni kuma an kira ni" "Na kammala karatu".

Read also

Rahoton EndSARS: HURIWA ta bukaci Buhari ya fatattaki Lai Mohammed kan karyar da ya zuga

Bayan na ki kwanciya da malamina, ya ce na zane shi, Dalibar da aka kora, ta kammala digiri daga baya
Bayan na ki kwanciya da malamina, ya ce na zane shi, Dalibar da aka kora, ta kammala digiri daga baya. Hoto daga @instablog9ja
Source: Instagram

An kore ta daga baya kuma aka kira ta

A yayin wallafa hoton ta tana daukar karatu, dalibar ta tuna lokacin da ta ke daukar jinjiri zuwa aji yayin da ta ke fama da kuncin rabuwar auren ta.

A yayin karatun, dalibar da ta kammala digiri a FUTO ta ce an kore ta amma daga bisani aka kira ta domin ta cigaba da karatun ta.

Yadda budurwar ta samu matsala da malamin ta

Ta bayar da labarin yadda malamin ta ya dinga bibiyar ta da lalata. Kamar yadda tace, a lokacin da ya ga ba zai samu abinda ya ke so ba, ya zarge ta da lakada masa mugun duka.

A wallafar ta: "Na kalla wannan hoton kuma na dinga kuka kamar karamar yarinya. Da jinjiri na ke zuwa aji kowacce rana yayin da ne ka fama da kuncin rabuwar aure na.

Read also

Jinsi ba shamaki bane: Injiniya mace 1 cikin maza ta sanar da gwargwamayar da ta sha duk da maraicinta

"Ina cikin haka ne aka kore ni daga makaranta. Malami na ya gaza ja na ya kwanta da ni, don haka yace na yi mishi mugun duka.
"A gaskiya na shiga mawuyacin hali a wannan lokacin, kalle ni a yanzu."

Jami'ar Ilorin ta kori dalibin dan aji hudu da ya lakadawa lakcararsa dukan kawo wuka

A wani labari na daban, hukumar gudanarwar jami’ar Ilorin ta kori wani dalibi mai suna Salaudeen Waliu Aanuoluwa na tsangayar nazarin ilmin halittu, bayan da aka same shi da laifin cin zarafin wata malamar jami’ar, Misis Rahmat Zakariyau.

A baya mun kawo muku rahoton yadda dalibin jami'ar dan aji hudu ya lakadawa lakcararsa dukan kawo wuka a harabar jami'ar saboda kin taimakonsa.

Wata sanarwa da Daraktan hulda na Jami’ar, Mista Kunle Akogun, ya fitar, ta bayyana cewa kwamitin ladabtarwa na dalibai ne ya yanke hukuncin.

Source: Legit.ng

Online view pixel