Da Dumi-Dumi: Sojoji sun fatattaki 'yan bindiga daga wani gari a Kaduna

Da Dumi-Dumi: Sojoji sun fatattaki 'yan bindiga daga wani gari a Kaduna

  • Dakarun sojojin Nigeria sun kori wasu 'yan bindiga da suka shiga garin Zango da nufin kai wa mutane hari
  • Lamarin ya faru ne a daren ranar Lahadi bayan sallar Isha'i misalin karfe 8 na dare inda 'yan bindigan suka yi wa garin zobe
  • Miyagun sun fara harbe-harbe bayan zagaye garin kawai sai dakarun sojojin suka iso garin suka fattatake su har wajen gari

Jihar Kaduna - Sojoji sun yi galaba a kan wasu 'yan bindiga da suka yi niyyar kai hari a garin Zongo da ke karamar hukumar Zangon Kataf a daren ranar Litinin a Kaduna.

Malam Isa Tela, wani mazaunin garin Zango ya shaida wa Daily Trust cewa mutane suna harkokinsu bayan sallar Isha'i misalin karfe 8 na dare, kwatsam suka fara jin harbe-harben bindiga.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun farmaki mazauna a Sokoto, sun hallaka mutane da yawa

Da Dumi-Dumi: Sojoji sun fatattaki 'yan bindiga daga wani gari a Kaduna
Sojoji sun fatattaki 'yan bindiga daga wani gari a Kaduna. Hoto: The Nation
Asali: Twitter

Ya ce hakan ya jefa mutane cikin fargaba a yayin da 'yan bindigan suka zagaye garin.

Ya ce:

"Mun fara jin harbe-harben bindigan ne misalin karfe 8 kusa da gidan mai na garin kafin suka zagaye garin daga kowanne bangare kafin sojojin suka iso suka tarwatsa su."

Ya ce babu wani labarin mutuwa ko rauni sakamakon harin a lokacin hada wannan rahoton.

Daily Trust ta ruwaito cewa an kashe mutane takwas a wasu hare-haren da aka kai a garuruwan Zangon Kataf a makon da ya gabata.

Rahoto: Masu ƙera wa Boko Haram bama-bamai sun koma dazukan Kudancin Kaduna

A baya, kun ji cewa shugabannin kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga Bakoura Buduma sun mayar da masu hada musu bama-bamai dazukan yankin kudanci Kaduna, a cewar wani rahoton da PRNigeria ta fitar.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bayan harin Islamiyya, Tsagerun yan bindiga sun sake mamaye Tegina, sun sace ma'aikata

A baya-bayan nan ne aka mayar da masu hada bama-baman da ake kira Amaliyyah a tsakin 'yan ta'addan, zuwa Rijana, Igabi da Chikun a yankin kudancin Kaduna.

Majiyoyi daga ciki sun ce kungiyoyin biyu na Boko Haram za su yi amfani da duwatsun da ke yankin a matsayin mabuya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel