Da duminsa: ISWAP sun sake kai hari, suna luguden wuta a Borno da kone gidaje

Da duminsa: ISWAP sun sake kai hari, suna luguden wuta a Borno da kone gidaje

  • Wasu da ake zargin mayakan ISWAP ne yanzu haka sun bude wuta a karamar hukumar Askira Uba da ke jihar Borno
  • An ruwaito yadda su ka babbaka gidaje a kauyen Dille da ke karamar hukumar yayin sabon hari da suka kai cikin kwanakin karshen mako
  • Majiyoyi sun nuna yadda mayakan suka afka kauyen da misalin karfe 5:30pm inda suka debe kayan abinci tare da tserewa da su

Borno - Wasu mayaka da ake zargin ‘yan ISWAP ne yanzu haka suna kai farmaki karamar hukumar Askira Uba da ke jihar Borno.

An samu rahotanni a kan yadda suka babbaka gidaje a kauyen Dille da ke karamar hukumar a wani hari da su ka kai kwanakin karshen mako, Daily Trust ta wallafa.

Da duminsa: 'Yan ta'addan ISWAP sun sake kai farmaki Borno, sun banka wa gidaje wuta
Da duminsa: 'Yan ta'addan ISWAP sun sake kai farmaki Borno, sun banka wa gidaje wuta. Hoto daga dailytrust.com
Asali: Original

Majiyoyi daban-daban sun shaida wa Daily Trust yadda ‘yan ta’addan suka kai farmaki kauyen da misalin karfe 5:30pm.

Majiyar ta shaida yadda suka balle shaguna sannan suka tsere da kayan abincin tare da kwasar na gidaje.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har yanzu dai ba a kammala bayar da rahoto akan yawan mutane da gidajen da lamarin ya shafa ba.

Lamarin ya faru ne bayan bai wuce kwana 2 da wani karon batta ya shiga tsakanin sojoji da mayakan ISWAP din ba a Askira Uba.

Sakamakon rikicin na karshen mako, mayakan sun halaka birgediya hanar Dzarma Zirkusu da wasu sojoji bayan sojojin sun halaka ‘yan ta’addan guda 50.

Kakakin rundunar sojin kasa, Birgediya janar Onyena Nwachukwu a wata takarda ya bayyana yadda rundunar soji ta 115 ta karade kauyen Leho da sauran kauyakun da ke kewaye da shi.

Ya kula da yadda sojojin su ka ga gawawwakin ‘yan ta’addan sannan su ka samo miyagun makamai wadanda mayakan su ka tsere su ka barsu.

Borno: Arangama ta da 'yan ta'addan ISWAP a kan titi, Malamin makaranta

A wani labari na daban, wani malamin makaranta da ke zama a karamar hukumar Damboa a jihar Borno ya bayyana yadda suka yi arangama da mayakan Islamic State in West Africa Province (ISWAP).

Malamin wanda ya bukaci a boye sunan sa, ya ce sun yi gaba da gaba da 'yan kungiyar yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa karamar hukumar Biu ta jihar a cikin kwanakin nan.

"Hankalinsu kwance suke yin komai kamar babu komai," yace.
"Direbanmu ya sanar da mu cewa kada mu tsorata lokacin da ya ga sun tunkaro mu. Suman zaune na yi amma a haka na samu kwarin guiwa. Sai na ji suna tambayata waye ni? Na sanar da su cewa ni dan kasuwa ne."

Asali: Legit.ng

Online view pixel