Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari za ta saka sabon haraji, 'Pure Water' zai koma N50 nan kusa

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari za ta saka sabon haraji, 'Pure Water' zai koma N50 nan kusa

  • Gwamnatin Najeriya a halin yanzu tana kammala wani shiri na sake dawo da haraji kan duk wani abin sha da ba na barasa ba a kasar
  • Shirin harajin kan abubuwan shaye-shaye da ba barasa ba an dakatar dashi ne a lokacin mulkin Ernest Shonekan a shekarar 1993
  • Masu masana'antu suna gargadin cewa sake dawo da harajin zai haifar da karuwar farashin abubuwan sha masu wadanda ba barasa ba

Kungiyar masu samar da ruwan sha ta Najeriya (WAPAN) ta bayyana cewa farashin ruwan ‘pure water’ na iya tashi daga N20 a yanzu zuwa N50 kan idan gwamnatin tarayya ta aiwatar da shirin haraji kan abubuwan shaye-shaye na yau da kullum.

Shugaban WAPAN na kasa, Eneri Odiri Jackson ne ya bayyana hakan a wani taron da aka gudanar a Legas. 'Yan Najeriya sun shaidi tashin farashin ruwa sau uku a cikin shekarar 2021; daga N5 zuwa N10 da kuma N20.

Kara karanta wannan

Luguden wutar jiragen NAF ya yi sanadin mutuwar shanu 1500 a Taraba

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari za ta kawo sabon haraji, 'Pure Water' zai koma N50 nan kusa
Ruwan leda da aka fi sani da pure water | Hoto: dailytrust.com

Kwamitin Majalisar Wakilai kan Kudi a watan Agusta 2021, ya yanke shawarar cewa za ta yi wa dokar Kudi kwaskwarima don dawo da haraji kan duk wani abin sha na yau da kullum.

Shugaban WAPAN na kasa, Eneri Odiri Jackson, ya ce aiwatar da haraji kan sinadarai da ake amfani da su wajen samar da ruwa zai yi tasiri ga tattalin arzikin kasar, kamar yadda DailyTrust ta ruwaito.

Jackson ya ce:

“Babu shakka farashin pure water zai tashi daga N20 zuwa kusan N50. Ina ba da shawarar cewa gwamnati ta yi nazari hekara mai zuwa, kafin a ci gaba da aiwatar da manufar."

Kungiyar masu samar da pure water na ATWAP sun koka kan raguwar mambobi a kungiyar tasu.

Mrs. Clementina Chinwe Ativie, shugabar ATWAP, ta ce mambobin kungiyar sun ragu da 16,000 sakamakon kalubalen tattalin arziki daban-daban, duk kuwa da cewa farashin pure water a kowace ya karu da fiye da 150% a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa har yanzu bata dage dakatarwar Twitter ba

Ta kuma bukaci a san yadda za a yi don a dakatar da sake dawo da haraji kan abubuwan sha.

Yunkurin dawo da harajin harajin ya fao ne daga Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam, Kanal Hammed Ali mai ritaya.

A cewarsa shigo da abubuwan sha da ba barasa ba da kuma barasa karkashin kulawar fitar da kaya zai rage illar dogaro da kudaden harajin mai da shigo da kaya.

Hakazalika, ya ce hakan zai taimaka wajen harkokin kiwon lafiya da muhalli tare da rage shan abubuwan sha masu cutarwa.

Shugaban Hukumar na Kwastam ya sake nanata bukatar masu ruwa da tsaki su tattauna kan matsalolin da masana’antun Najeriya suka bayyana.

Yadda Najeriya ta shigo da kifin sama da N100bn daga kasashe 10 na waje cikin wata 6

A wani labarin, duk da yawan ruwa da ake dashi, Najeriya a cikin watanni shida na farkon shekarar 2021 ta kashe Naira biliyan 123.8 wajen shigo da kifi daga waje, Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana.

Kara karanta wannan

Majalisa ta kawo dabarar hana magudin zabe, za a rika aiki da na’ura wajen tattara kuri’u

Bayanan na kunshe ne a cikin rahoton kididdigar Kasuwancin Kayayyakin Waje na NBS da ta buga a shafin yanar gizon ta.

Rahoton ya ce an shigo da kifi da ya kai Naira biliyan 48.28 a zangon farko sannan kuma an shigo da na Naira biliyan 75.44 a zango na biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel