Luguden wutar jiragen NAF ya yi sanadin mutuwar shanu 1500 a Taraba

Luguden wutar jiragen NAF ya yi sanadin mutuwar shanu 1500 a Taraba

  • A kalla shanu 1500 ne suka halaka a garin Takum da ke jihar Taraba sakamakon luguden wutar da jiragen NAF suka yi musu
  • Makiyaya kuma Fulanin yankin sun tabbatar da cewa mummunan al'amarin ya auku ranakun Laraba ne da Alhamis
  • Mazauna yankin sun sanar da yadda wasu shanun suka raunata, lamarin da yasa naman shanu yayi arha a jihar Taraba

Taraba - Kusan shanu 1500 ne aka rasa sakamakon luguden ruwan wutar da sojojin sama suka yi a wata rugar Fulani da ke karamar hukumar Takum ta jihar Taraba.

Daily trust ta tattaro cewa, jiragen yakin sun kaddamar da luguden wutan kan gidajen Fulani makiyaya da ke wurin Kashinbila da Tor Donga a ranakun Laraba da Alhamis inda suka kashe shanu 1500.

Luguden wutar jiragen NAF ya yi sanadin mutuwar shanu 1500 a Taraba
Luguden wutar jiragen NAF ya yi sanadin mutuwar shanu 1500 a Taraba. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

An gano cewa, sun saki ruwan wutan ne wurin karfe 11 na safe da kuma hudu na yammacin Laraba da Alhamis.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An bindige mutane biyar yayin da jihar Imo ta sake daukar zafi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani wanda lamarin ya shafa mai suna Sadu Saidu, ya sanar da Daily Trust cewa ya rasa kusan shanu guda dari da ashirin yayin da dan uwansa ya rasa shanu dari da biyar.

"Za mu jagoranci shanunmu zuwa wurin kiwo kenan lokacin da muka ji karar jirgi kuma suka fara barin wuta. Mun tsere tare da tsayawa karkashin manyan itace kuma a take suka kashe mana shanu dari bakwai," Sadu yace.

Ya ce wannan jirgin ne ya sake dawowa a rana ta biyu inda ya kai farmakin ruga biyu tare da kashe shanu kusan dari bakwai da hamsin.

Wani wanda abun ya shafa mai suna Musa, ya ce baya da kashe shanun, da yawa daga cikin shanunsu sun raunata kuma sun watsar da su a garin Takum.

Ya ce lamarin ya sa daruruwan Fulani sun kada shanunsu zuwa Kamaru, Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Yadda aka kusa halaka zababben gwamnan Anambra saura wata 8 zabe

Wani mazaunin Takum mai suna Yakubu Rabiu, ya ce naman shanu ya yawaita a Takum kuma ana ta siyar da shi cikin arha.

Mai Magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Taraba, Usman Abdullahi, ya tabbatar da aukuwar al'amarin amma ya ce a jihar Binuwai ne lamarin ya faru ba a Taraba ba.

Yobe: Jama'ar da jirgin NAF ya yi wa luguden wuta suna bukatar diyya

A wani labari na daban, iyalan wadanda mummunan lamarin da ya faru a jihar Yobe da su sakamakon luguden wutan da jirgin NAF ya so yi kan 'yan ta'addan Boko Haram, sun bukaci gwamnatin tarayya da ta biya su diyya.

Sun alakanta bukatarsu da dalilin cewa, gwamnati a kowanne mataki a Najeriya ba ta cika biyan diyya ba ga jama'a da aka yi wa barna, Daily Trust ta ruwaito.

Daga ciki mutum takwas da suka rasu, tsoffafi uku da wata mata wadanda suka bar kananan yara. Akwai yara kanana hudu da suka rasa rayukansu da kuma wasu gidaje da suka kone.

Kara karanta wannan

Lamari ya yi muni yayin da matasa suka ba hammata iska, suka datse hannayen juna

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel