Meyasa kowace matsala ta tare a yankin Arewa, Attahiru Jega ya caccaki shugabannin Najeriya

Meyasa kowace matsala ta tare a yankin Arewa, Attahiru Jega ya caccaki shugabannin Najeriya

  • Tsohon shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega, yace masu rike da madafun iko a Najeriya ba su da ilimin kaiwa matakin da suke
  • Jega yace a halin da ake ciki yanzun kowace matsala tana taso wa ne daga Arewa, Talauci rashin aikin yi da sauransu
  • A cewarsa Najeriya na da wasu kalan shugabanni da basu da son rai, amma suna mance wa da yankin da suka fito

Katsina - Tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta, Farfesa Attahiru Jega, yace shugabannin Najeriya ba su da ilimin kasancewa a matakin da suke sam.

Da yake jawabi a wurin lakcar Maitama Sule, wanda kungiyar ɗaliban Arewa SW-CNG ta shirya a Katsina, ranar Litinin, tsohon shugaban INEC ɗin ya alaƙanta matsalolin Najeriya da rashin jagoranci mai kyau.

Kara karanta wannan

Lamari ya yi zafi, dattawan Arewa sun zauna don neman mafita ga matsalolin Arewa

A rahoton Dailytrust, Jega yace Najeriya ba ta yi dacen shugabanni ba idan ana magana kan gudanar da ayyukan cigaban ƙasa.

Attahiru Jega
Meyasa kowace matsala ta tare a yankin Arewa, Attahiru Jega ya caccaki shugbaannin Najeriya Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Meyasa kowace matsala ta tare a Arewa?

Farfesa Jega, wanda shine shugaban taro, yace matsalar talauci, zaman kashe wando tsakanin matasa, rashin tsaro, rashin zuwa makaranta, auren wuri da sauran matsalolin da suka shafi lafiya duk sun tattaru a Arewa.

This Day ta rahoto Jega yace:

"Duk wasu manyan matsaloli kamar rashin tsaro, auren wuri, matsalolin da suka shafi lafiya, yara masu gararamba a titi, rashin aikin yi duk sun mamaye yankin Arewa."
"Duk wani abu mara kyau, ko wata matsala zaka ga ta fito ne daga arewacin Najeriya, to meyasa haka? Wannan shine babban abin tambaya."

Meyasa muke tunawa da jagororin mu na baya?

Kara karanta wannan

Za a kai shugaban cibiyar da ya yi shekara 18 yana cin albashi da takardun bogi kotu

Farfesa Jega ya bayyana cewa a halin yanzun sai dai mutanen arewa su cigaba da bikin tuna manyan mutane irinsu, Saradauna, Maitama Sule, Isa Kaita da sauransu.

"Waɗan nan mutanen sun jaogaranci arewa kuma sun kare martabarta, sun tabbatar da Arewa ta cigaba dai-dai karfinta da matsayinsu na shugabanni."
"Yayin da muke tuna gudummuwar waɗan nan bayin Allah da suka shuɗe, ya dace mu tambayi kan mu, wane irin jagoranci muke samu daga Arewa?"

A wani labarin kuma Shugaban majalisar malamai na kungiyar Izala ya magantu kan tsarin mulkin karba-karba a 2023

Sheikh Sani Yahaya Jingir yace babu wanda ya isa ya siyar da kuri'un mutane da sunan karba-karba a 2023.

Shehin Malamin ya kira tsarin da wani abu mai kama da caca, kuma a cewarsa mutane kada su yarda da shi kwata-kwata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel