Labari da duminsa: An rufe gidan casun Obi Cubana da ke Abuja har sai abinda hali ya yi

Labari da duminsa: An rufe gidan casun Obi Cubana da ke Abuja har sai abinda hali ya yi

  • An rufe wani kulob mallakar Obinna Iyiegbu da aka fi sani da Obi Cubana a babban birnin tarayya Abuja
  • A cewar mahukunta kulob din, an rufe gidan casun ne sakamakon mutuwa da wata mata yi bayan lankarki ya ja ta
  • Abin bakin cikin ya faru ne a ranar Lahadi, 14 ga watan Nuwamba, hakan yasa aka rufe kulob din har zuwa wani lokaci nan gaba

FCT, Abuja - An rufe kulob, wato gidan casu na Hustle and Bustle mallakar babban dan kasuwa Obinna Iyiegbu da aka fi sani da Obi Cubana, Daily Trust ta ruwaito.

Mahukunta a kulob din sun rufe shi ne bayan wata budurwa da ta tafi casu ta mutu sakamakon wutan lankarki da ja ta.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba.

Read also

An shigar da Hafsat Barauniya kotu kan amsar kudi amma taki yin aikin

Labari da duminsa: An rufe gidan casun Obi Cubana da ke Abuja har sai abinda hali ya yi
An rufe gidan casun Obi Cubana da ke Abuja har sai abinda hali ya yi. Hoto: @obi_cubana
Source: Instagram

Da ya ke tabbatar da lamarin, kulob din ta ce an dakatar da ayyuka 'har zuwa wani lokaci' a nan gaba.

Sanarwar da kungiyar ta fitar ya ce:

"Mun rufe har zuwa wani wuri nan gaba. Hakan ya faru ne dalilin rasuwar wata mata. Muna matukar bakin faruwar lamarin kuma muna bukatar lokaci mu yi zaman makoki."
"Muna mika ta'aziyya ga iyalan wanda ta rasu. Allah ya jikanta da rahama. Muna taya iyalanta alhinin rashin ta. Ku yi hakuri da mu a yayin da muke juyayin rashin ta."

EFCC ta saki Obi Cubana, attajiri mai facaka da dukiya

A baya, Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta sako attajirin mai facaka da dukiya, Obinna Iyiegbu, da aka fi sani da Obi Cubana.

Read also

El-Rufai na shan caccaka bayan da aka gano ya saba umarnin Buhari, ya yi amfani da Twitter

Instigator PH, abokin aikinsa ne ya wallafa labarin sakinsa a shafinsa na dandalin sada zumunta ta Instagram a ranar Talata.

Ya rubuta:

"Mun gode Yesu!! @obi_cubana ya kubuta. Muna da Yesu. Wannan rawa ce ga dukkan masoya na. Ina kaunar ku dukkan ku."

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel