El-Rufai na shan caccaka bayan da aka gano ya saba umarnin Buhari, ya yi amfani da Twitter

El-Rufai na shan caccaka bayan da aka gano ya saba umarnin Buhari, ya yi amfani da Twitter

  • Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya sha caccaka bayan da aka gano ya yi amfani da Twitter
  • El-Rufai dai ya je shafinsa na Twitter a ranar Laraba, 10 ga watan Nuwamba domin mayar da martani ga wani jinjina da aka masa a matsayin tsohon ministan Abuja
  • Sai dai ganin gwamnan a dandalin ya ba yan Najeriya da dama mamaki duba ga cewar ya saba umurnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na haramta amfani da Tuwitar

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai ya bayyana a dandalin sada zumunta ta Twitter a ranar Laraba, 10 ga watan Nuwamba, 2021, duk da haramcin da gwamnatin tarayya ta sanyawa kafar sadarwar, jaridar Punch ta rahoto.

Saba umurnin shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan yayi duk da kusancin da ke tsakaninsu ya sanya 'yan Najeriya yi masa wankin babban bargo.

Kara karanta wannan

Hotunan tsohon mataimakin gwamna a Najeriya da ya koma noman doya shi da matarsa

El-Rufai na shan caccaka bayan da aka gano ya saba umarnin Buhari, ya yi amfani da Twitter
El-Rufai na shan caccaka bayan da aka gano ya saba umarnin Buhari, ya yi amfani da Twitter Hoto: Punch
Asali: UGC

Sahara Reporters ta kuma rahoto cewa gwamnan ya je shafin nasa ne a wannan rana don mayar da martani ga wani mutum da ya jinjinawa ayyukansa a matsayin tsohon ministan birnin tarayya.

Taiwo Ajakaye da shafin twitter @dmightyangel ya rubuta:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Na so ace za mu samu irin @elrufai da yawa a siyasa. Mutumin ya bar FCT amma har yau, birnin tarayya bata sake samun wani minista da yayi ko kusa da abun da El-Rufai yayi ba ta bangaren jajircewa, gudanar da mulki, aiki da mayar da hankali, shekaru 14 da suka gabata fa.”

Da yake mayar da martani ga rubutun, gwamnan ya rubuta:

"Akwai karin gishiri a wannan yabon @dmightyangel amma nagode da wasu daga cikin kalaman karfafa gwiwar. Allah ya albarkaci kasarmu.– @elrufai”

A bangaren sharhi, @dexybaba ya tambayi gwamnan ko yana amfani da boyayyar hanyar sadarwa ta VPN ne, sai ya yi masa martani da cewar baya cikin kasar kuma cewa yana iya wallafa a twitter na dan lokacin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa har yanzu bata dage dakatarwar Twitter ba

Hakazalika jagoran zanga-zangar #EndSARS kuma mai rajin kare hakkin dan adam, Rinu Oduala ya yi saurin sanar da gwamnan a bangaren sharhi cewa:

"Wuri guda da mutum ke da yancin yin magana shine a wajen Najeriya."

Da yake martani ga Rinu, El-Rufai ya jadadda cewa:

"Ba daidai bane @SavvyRinu! Twitter da 'yancin magana tamkar karin gishiri a miya ne. Yancin magnganu da dama na nan tun da dadewa kuma ko babu Twitter, sannan zai ci gaba da kasancewar har bayan nan!! Ka ji dadinka.”

Wata mai amfani da Twitter, @ogbuebunu, itama ta ce:

"Abun kunya. Yin rubutu a twitter ta hanyar fakewa da cewar kana wajen kasar ya nuna rashin da'a. Mutum zai yi zaton zai tsaya tsayin daka tunda jam'iyyarsa ce ta haramta Twitter. Koda dai, har yanzu shi dan siyasar Najeriya ne. Babu mutunci ko kadan."

Hakazalika Aisha Yesufu ta caccaki gwamnan kan amfani da dandalin a wajen kasar, yayin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan jam'iyyar APC kamarsa ya haramta amfani da Twitter a Najeriya.

Kara karanta wannan

Charles Soludo: Muhimman abubuwa 10 da ya dace ku sani game da zababben gwamnan Anambra

Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa har yanzu bata dage dakatarwar Twitter ba

A wani labarin, gwamnatin tarayya ta ce ba a dage dakatarwar da aka yi wa shafin Twitter ba saboda kamfanin ya cika sharudda 10 ne kacal daga cikin 12 da aka gindaya masa.

Sai dai gwamnatin ta kara da yi wa ‘yan Najeriya fatan cewa lokaci ya yi da za a shawo kan duk wata matsala ta Twitter.

Hakazalika, ta bayyana cewa dakatar da shafin Twitter ba shi da alaka da batutuwan da suka shafi shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng