Yanzu-yanzu: EFCC ta saki Obi Cubana, attajiri mai facaka da dukiya

Yanzu-yanzu: EFCC ta saki Obi Cubana, attajiri mai facaka da dukiya

  • Hukumar EFCC ta saki Obinna Iyiegbu, da aka fi sani da Obi Cubana bayan ya shafe kimanin awa 24 a ofishinta
  • EFCC ta kama Obi Cubana ne kan zarginsa da hallastawa kansa kudaden haramun da kuma rashin biyan haraji
  • Amma daga bisani hukumar ta EFCC ta bada belinsa bayan ya cika wasu ka'idoji da ta gindaya masa

Abuja - Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta sako attajirin mai facaka da dukiya, Obinna Iyiegbu, da aka fi sani da Obi Cubana.

Instigator PH, abokin aikinsa ne ya wallafa labarin sakinsa a shafinsa na dandalin sada zumunta ta Instagram a ranar Talata.

Yanzu-yanzu: EFCC ta saki Obi Cubana, attajiri mai facaka da dukiya
EFCC ta saki Obi Cubana, attajiri mai facaka da dukiya. Hoto: Obi Cubana
Source: Instagram

Read also

Yanzu-Yanzu: Wani gini mai hawa-hawa ya sake ruftawa a jihar Legas

Ya rubuta:

"Mun gode Yesu!! @obi_cubana ya kubuta. Muna da Yesu. Wannan rawa ce ga dukkan masoya na. Ina kaunar ku dukkan ku."

Ya kuma wallafa wani rubutu da ke cewa:

"Labari da duminsa. Obi Cubana ya kubuta. Na tabbatar da hakan, ni ne kadai Instigator. Ku dakaci kyautan kudi."

Shima Obi Cubana ya tabbatar da sakinsa a wani wallafa a shafinsa na Instagram yana mai cewa 'bai karaya ba'.

Majiyoyi sun bayyana cewa an bada belinsa ne.

Hukumar yaki da rashawar ta kama shi ne a ranar Litinin ta masa tambayoyi kan zargin hallasta kudin haram da kuma kin biyan haraji.

Yan Najeriya da dama sun bayyana ra'ayoyinsu game da kama Cubana da dandalin sada ciki har da jarumai da mawaka.

Tunda farko, 2 Face, Peter Okoye, Ubi Franklin da Cubana Chief Priest sun nuna goyon bayansu ga attajirin ta hanyar amfani da hashtag #FreeObiCubana.

Kazalika, Dan Yusuf Bichi, shugaban hukumar yan sandan farin kaya, DSS, ya yabi Cubana inda ya kira shi 'mutumin kirki'

Read also

Kamen Obi Cubana: 'Dan DG na DSS ya caccaki EFCC, ya ce "karnukan 'yan siyasa" ne

Yan sanda sun kama abokan aikinsu suna ƙwacewa wani matafiyi kuɗi

A wani rahoton, rundunar ‘yan sanda ta kama wasu jami’in ta da laifin kwacen kudin daga hannun wani matafiyi, Victor Agunwah bayan ya kai korafi wurin Rabiu Hussaini, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Imo.

The Cable ta ruwaito yadda ya kai karar ne inda ya bayyana cewa dan sandan ya kwace N60,000 a wurin sa inda ya bukaci ya tura masa ta POS.

A cewar sa dan sandan ya cutar da shi da sauran wadanda su ke cikin motar inda ya tilasta ma sa tura ma sa kudin bisa ruwayar The Cable.

Source: Legit.ng

Online view pixel