Matsalar tsaro a Najeriya ta zo karshe da zaran yan majalisu sun amince da kudirin mafarauta, Yahaya Bello

Matsalar tsaro a Najeriya ta zo karshe da zaran yan majalisu sun amince da kudirin mafarauta, Yahaya Bello

  • Gwamnan Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya bayyana cewa matukar yan majalisu suka amince da kudrin mafarauta to za'a samu sauki
  • A cewarsa mafarauta na taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da matsalar tsaro a jihar ta Kogi, domin suke ceto jami'an tsaro
  • Bello ya kuma gode wa ƙungiyar mafarautan bisa nuna masa goyon baya a kokarin da yake na neman shugabancin Najeriya

Abuja - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya roki yan majalisun tarayya su gaggauta amincewa da kudirin mafarauta 2020 ya zama doka.

The Cable tace kudirin wanda ya tsallake karatu na ɗaya da na biyu a dukka majlisun tarayya biyu, sanata mai wakiltar Ekiti ta kudu, Biodun Olujimi, shine ya gabatar da shi.

Yahaya Bello
Matsalar tsaro a Najeriya ta zo karshe da zaran yan majalisu sun amince da kudirin mafarauta, Yahaya Bello Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Yayin ya karbi bakuncin ƙungiyar mafarauta ta Najeriya a Abuja ranar Asabar, Bello yace mafarauta zasu taka rawar gani wajen taimaka wa FG a yaƙin da take da matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Hotunan shugaban ɗalibai da masu tsaronsa da suka ɗauki hankula: Jami'ar FUD ta bayyana gaskiyar lamari

Ko wane kokari mafarauta suke a jihohi?

A cewar gwamnan ɗaya daga cikin manyan dalilin da yasa gwamnatinsa a Kogi ta samu nasarar dakile aikata manyan laifukan ta'addanci shine amfani da mafarauta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan yace:

"Zan roki majalisar tarayya ta yi saurin amincewa da kudirin mafarauta ya zama doka domin hakan zai bamu damar ɗaukar ku aiki baki ɗaya."
"Kuna ganin yadda mafarauta suke yi a jihar Kogi, wani lokacin ma suke zuwa su ceto jami'an tsaro idan rana ta baci. Idan kowane inci na ƙasa kuna wurin, to zaku kare shi.
"Idan kuwa muka kare kowane inci na kasa, to kauyukan mu zasu zauna lafiya, kananan hukumomi, jihohi, hatta ƙasar mu zata samu zaman lafiya."

Daga ƙarshe gwamnan ya gode wa mafarautan bisa nuna goyon bayansu ga takararshi a 2023, tare da tabbatar musu da cewa za'a tafi da su.

Kara karanta wannan

Nasrun minallah: Dakarun Sojoji sun tarwatsa mayakan Boko Haram/ISWAP a kan hanyar Maiduguri

A wani labarin na daban kuma Mutum 6 sun mutu yayin da wasu tsagerun yan bindiga suka sake kai sabon hari jihar Katsina

Wani sabon hari da miyagun yan bindiga suka kai jihar Katsina ya yi sanadin mutuwar mutum 6, wasu da dama sun jikkata.

Mazauna yankin sun tabbatar da cewa maharn sun shiga ƙauyen Gwarjo, ƙaramar hukumar Matazu da daddare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel