Hotunan shugaban ɗalibai da masu tsaronsa da suka ɗauki hankula: Jami'ar FUD ta bayyana gaskiyar lamari

Hotunan shugaban ɗalibai da masu tsaronsa da suka ɗauki hankula: Jami'ar FUD ta bayyana gaskiyar lamari

  • Jami'ar Tarayya ta Dutse, FUD, ta yi karin bayani game da wasu hotunan shugaban daliban makarantar tare da masu tsaro
  • Hotunan dai sun bazu a dandalin sada zumunta inda mutane ke mamakin ganin yadda aka yi wa shugaban daliban zuwa aji cikin mota da masu tsaro
  • Mahukunta daga makarantar sun yi karin haske inda suka ce an dauki hoton ne a lokacin da daliban wani shirin wayar da kai amma ba haka ya ke zuwa aji ba a kullum

Jihar Jigawa - Wasu hotuna da suka bazu a dandalin sada zumunta sun nuna shugaban Ƙungiyar Ɗalibai na Jami'ar Tarayya da ke Dutse a Jigawa sun nuna ya iso aji tare da tawaga biye da shi.

Hotunan da suka fito a ranar Alhamis, sun nuna shugaban na SUG ya a makarantar cikin motar ƙirar Mercedes Benz tare da masu tsaronsa sanye da baƙaken suit.

Kara karanta wannan

Gumi ya caccaki 'yan aware: Igboho da Kanu ne suka kunna wutar rikicin Fulani a kudu

Hotunan shugaban ɗalibai da masu tsaronsa da suka ɗauki hankula: Jami'ar FUD ta bayyana gaskiyar lamari
Hotunan shugaban ɗalibai da masu tsaronsa da suka ɗauki hankula: FUD ta bayyana gaskiyar lamari. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Ana kyautata zaton masu tsaronsa su shida dukkansu ɗalibai ne a jami'ar.

Hotunan sun janyo cece-kuce daga bangarori da dama a dandalin sada zumunta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Inibehe Effiong, lauya mai kare hakkin bil adama, ya wallafa hotunan a shafinsa na Facebook yana cewa, 'Nigeria babban misali ne na yadda za a iya ɗora ƙasa kan turbar lalacewa'.

Mahukunta a makarantar sunyi ƙarin haske

Babban Jami'in Watsa Labarai na FUD ya yi fashin baki

Abdullahi Yahaya Bello, babban jami'in watsa labarai na Jami'ar Tarayya da ke Dutse, FUD, ya bayyana gaskiyar labari game da hotunan.

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce an dauki hotunan ne a lokacin da daliban ke bikin su, suke nuna yadda ake samar da tsaro ga muhimman mutane kuma aka yi misali da shugaban na FUD.

Kara karanta wannan

Nasrun minallah: Dakarun Sojoji sun tarwatsa mayakan Boko Haram/ISWAP a kan hanyar Maiduguri

Ya ce ba zai yiwu dalibai su yi watsi da karatunsu ba domin kawai su yi wa shugban SUG rakiya zuwa aji.

Jami'ar tana bada muhimmanci wurin bawa daliban horaswa don haka za zai yi wu ta sanya ido a rika yin abubuwan da basu dace ba.

Hakazalika, Osita Nicholas, malami da ya ce a makarantar ya ke aiki ya ƙaryata zargin ake yi na cewa a kullum haka shugaban na FUD ke zuwa aji.

A cewarsa, daliban tsangayar nazarin laifuka da tsaro ne suke wani shiri na wayar da kan al'umma a lokacin da aka ɗauki hotunan.

Ya shaidawa The Cable cewa:

"A kowanne shekara, ɗaliban tsangayoyi daban-daban sukan ware ranaku na musamman don wayar da kan mutanen kan abinda karanta."

Daliban mu masu nazarin Criminology and Security Studies suma suna nasu.

Suna wayar da al'umma game da batutuwan da suka shafi tsaro har su kan nuna matakan tsaron a aikace. Su kan yi aiki tare da jami'an tsaro a kofar shiga jami'a, su su kammala da taro.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Jami’an tsaro sun hana lauyan Kanu, yan jarida da shugabannin Ibo shiga harabar kotu

Abin da aka gani a hotunan ɗalibai ne ke bada tsaro na musamman ga shugaban daliban na rana guda kawai. A ranar ne kawai. Kowa zai koma ya cigaba da zuwa aji kamar yadda ya saba.

Abin da yasa har yanzu Nigeria bata zama ƙasaitacciyar ƙasa ba, Ministan Buhari

A wani labarin daban, Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ce har yanzu Nigeria bata cimma babban matakin da ake sa ran ta kai ba a lokacin samun 'yanci saboda an yi watsi da irin halayen mazajen jiya da suka kafa kasar.

Ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja wurin wani taro da kungiyar 'Yan Kabilar Igbo ta shirya don karrama Rear Admiral Godwin Kanu Ndubuisi (mai ritaya), Daily Trust ta ruwaito.

Onu ya ce ya zama dole 'yan Nigeria su zama masu gaskiya, aiki tukuru da riko da halaye na gari idan suna son ganin kasar ta zama tauraro tsakanin sauran kasashe.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel