Na jinjinawa bajintarsu: Buhari ya yi makokin sojojin da mayakan ISWAP suka kashe

Na jinjinawa bajintarsu: Buhari ya yi makokin sojojin da mayakan ISWAP suka kashe

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alhinin mutuwar Birgediya Janar Dzarma Zirkusu da wasu dakarun sojoji da suka rasa ransu a wani artabu da mayakan ISWAP
  • 'Yan ta'addan sun kashe dakarun sojojin ne a wani hari da suka kai masu a garin Askira da ke karamar hukumar Askira Uba ta jihar Borno
  • Buhari ya mika sakon ta'aziyyarsa ga shugaban hafsan soji da iyalan mamatan sannan ya jinjina wa kokarin dakarun da suka sadaukar da ransu wajen kare kasar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna bakin ciki a kan mutuwar Birgediya Janar Dzarma Zirkusu da sauran sojojin wadanda mayakan kungiyar ta'addanci na ISWAP suka halaka, jaridar Punch ta rahoto.

'Yan ta'addan sun kashe dakarun sojojin ne a wani kwantan bauna da suka kai masu a yankin Askira da ke karamar hukumar Askira Uba ta jihar Borno, a ranar Asabar, 13 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Hotuna da sunayen jaruman Sojojin da aka kashe a artabu da yan ta'adan ISWAP

Na jinjina bajintarsu: Buhari ya yi makokin sojojin da kungiyar ISWAP ta kashe
Na jinjina bajintarsu: Buhari ya yi makokin sojojin da kungiyar ISWAP ta kashe Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Shugaban kasar a cikin wata sanarwa daga mai bashi shawara kan harkokin labarai, Garba Shehu, ya ce mamatan sun yi gagarumin sadaukarwa mai tsada da ba a saba gani ba a yayin da suke kokarin taimakawa ‘yan uwansu wajen yaki da ‘yan ta’adda.

Buhari ya mika sakon ta'aziyyarsa ga shugaban hafsan sojin kasa, Laftanal Janar Faruk Yahaya da kasar baki daya. Hakazalika ya bukaci iyalan mamatan da su amshi sakon ta'aziyyarsa, rahoton Daily Trust.

Buhari ya ce:

"Najeriya ta yi rashi na jaruman sojoji. Na jinjinawa bajintarsu. Allah ya ji kansu da Rahama. Janar Zirkusu ya bar mu cikin bakin ciki da bacin rai. Ba za a taba mantawa da sunansa na soja ba.
"Ina rokon Allah madaukakin sarki ya baka da iyalan mamatan karfin gwiwar jure wannan babban rashi."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An kashe mayakan ISWAP da yawa yayin da artabunsu da sojoji ya shiga awa na 8

Hukumar Sojin Najeriya ta tabbatar da kisan Birgediya Janar a harin kwantan baunar ISWAP

A baya mun kawo cewa hukumar Sojin Najeriya tabbatar da kisan Birgediya Janar Dzarma Zirkushu, Kwamandan rundunar 28 Task Force Brigade, dake Chibok, jihar Borno, Arewa maso gabas.

Yan ta'addan sun kashe Janar din tare da wasu jami'ansa uku, yayinda suke hanyar =su ta zzuwa kai dauk ga Sojoji a kauye Bungulwa dake kusa Askira Uba.

Kakakin hukumar Sojin Najeriya, Onyeama Nwachukwu, ya sanar da hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar, rahoton DailyNigerian.

Asali: Legit.ng

Online view pixel