Hotuna da sunayen jaruman Sojojin da aka kashe a artabun Soji da yan ta'adan ISWAP

Hotuna da sunayen jaruman Sojojin da aka kashe a artabun Soji da yan ta'adan ISWAP

Hukumar Sojin Najeriya tabbatar da kisan Birgediya Janar Dzarma Zirkushu, Kwamandan rundunar 28 Task Force Brigade, dake Chibok, jihar Borno, Arewa maso gabas.

Kakakin hukumar Sojin Najeriya, Onyeama Nwachukwu, ya sanar da hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar.

Yayinda ya bayyana sunan kwamandan, ba'a san sunayen sauran jami'an Sojojin ba.

Sahara Reporters ta ce ta samu sunaye da hotunan sauran Sojojin:

An bayyana sunayensu matsayin; Ahmed S, Israel Ladoke, Mathew da Victor.

Hotuna da sunayen jaruman Sojojin da aka kashe
Hotuna da sunayen jaruman Sojojin da aka kashe a artabun Soji da yan ta'adan ISWAP Hoto: HqNigerian Army
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hotuna da sunayen jaruman Sojojin da aka kashe a artabun Soji da yan ta'adan ISWAP
Hotuna da sunayen jaruman Sojojin da aka kashe a artabun Soji da yan ta'adan ISWAP
Asali: Facebook

Hotuna da sunayen jaruman Sojojin da aka kashe a artabun Soji da yan ta'adan ISWAP
Hotuna da sunayen jaruman Sojojin da aka kashe a artabun Soji da yan ta'adan ISWAP
Asali: Facebook

An yi artabu tsakanin Soji da yan ta'addan ISWAP

Mun kawo muku cewa 'Yan ta'addan ISWAP sun yi musayar wuta da sojoji a wani sansanin soja da ke karamar hukumar Askira/Uba a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An kashe mayakan ISWAP da yawa yayin da artabunsu da sojoji ya shiga awa na 8

Wasu mazauna sun ce sun hango mayakan na ISWAP a cikin wani dogon ayarin motocin bindigu a hanyar Ngude zuwa Askira, da sanyin safiyar yau.

Wani jami'in leken asiri ya bayyanaewa PRNIgeria cewa,

"Yan ta'addan ISWAP da suka kai hari Askira Uba sun lalata hatsumiyar sadarwa da bindigogi da wasu makamai dake hannunsu."
"An kashe kwamandan Soji daya a harin kwantar baunar yayinda yake jagorantar rundunar kai dauki. Hakazalika an kashe wasu Soji."
"Wasu yan ta'addan daban kuma sun kai hari kauyen Mulai, kusa da Maiduguri inda suka sace Shanu yayinda wasu suka lalata hatsumiyar sadarwa a Buni Yadi jihar Yobe kuma suka sace Janareto da magunguna."

Asali: Legit.ng

Online view pixel