Ba zan yarda da wannan zaben ba, kawai magudi akayi: Dan takaran APC a zaben Anambra

Ba zan yarda da wannan zaben ba, kawai magudi akayi: Dan takaran APC a zaben Anambra

  • Dan takaran jam'iyyar All Progressives Congress APC ya bayyana cewa bai yarda da sakamakon zaben jihar da INEC ta sanar ba
  • Kwamitin yakin zaben Andy Uba tace bai zai yiwu ace duk da sauya shekar da manyan jigogin APGA sukayi zuwa APC, su fadi zabe ba
  • Dan takaran jam'iyyar APC ne ya zo na uku a zaben gwamnan jihar Anambra bisa sanarwar hukumar INEC

Anambra - Kwamitin yakin zaben Sanata Andy Uba ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan jihar Anambra da hukumar zabe ta kasa watau INEC ta sanar ranar Laraba.

Kwamitin tace babu abinda ya faru a zaben nan illa magudi da rufa-rufa kuma ba haka al'ummar jihar suka so ba.

Ambassador Jerry Ugokwe, a jawabin da ya saki ranar Alhamis a madadin kwamitin ya bayyana cewa Hukumar INEC ta yiwa dan takaran APC, Sanata Andy Uba, murdiya ne kawai.

Read also

Duk da inkarin APC, INEC za ta ba Soludo takardar shaidar lashe zaben Anambra

Ba zan yarda da wannan zaben ba, kawai magudi akayi: Dan takaran APC a zaben Anambra
Ba zan yarda da wannan zaben ba, kawai magudi akayi: Dan takaran APC a zaben Anambra
Source: UGC

A jawabin da Legit ta samu, ya bayyana yadda na'urar tantance masu zabe taki aiki a wurare daban-daban.

Yace:

"Wannan zabe cike yake da rashin gaskiya, tsoratar da mutane, hana mutane zabe don baiwa APGA nasara."
"Misali,a rumfunan zaben da na'urar BVAS taki saiti, INEC ta gudanar da zabe ba tare da tantance mutane ba. Akwai wurare da dama inda INEC ta sanar da sakamakon zabe wanda adadin ya wuce adadin wadanda aka tantance."
"Ba zai hankaltu ace dan takaranmu wanda ya samu kuri'u 200,000 a zaben fidda gwanin APC ya samu kuri'u 43,000 ba."
"Hakazalika da ban mamaki a ce APGA da ta rasa kimanin kashi 80% na jigoginta da suka koma APC ta ci zabe."

A cewar kwamitin, mutanen da suka rage a APGA basu wuce Gwamnan jihar Willie Obbiano, Farfesa Charles Soludo da iyalansu ba.

Source: Legit.ng

Online view pixel