Dalilin da yasa na kashe dan jaridar Vanguard - Wanda ake zargi

Dalilin da yasa na kashe dan jaridar Vanguard - Wanda ake zargi

  • Wanda ake zargi kan kisan dan jaridar Vanguard, Tordue Salem, ya bayyana dalilinsa na kashe marigayin
  • Clement Itoro wanda ya kasance direban motar kasuwa, ya ce ya ki tsayawa bayan ya banke Salem ne saboda ya yi zaton shi dan fashi ne
  • Itoro ya ce yankin Mabushi, inda ya banke marigayi dan jaridar sanannen wajen masu fashi da makami ne don haka sai ya tsorata

Abuja - Clement Itoro, dan shekara 29 da yan sanda suka kama bisa zargin kashe dan jaridar Vanguard, Tordue Salem, ya bayyana dalilinsa na aikata laifin.

A cewar Itoro, ya kashe marigayin ne ta hanyar banke shi da motarsa sannan ya gudu saboda ya yi zaton shi barawo ne.

Dalilin da yasa na kashe dan jaridar Vanguard - Wanda ake zargi
Dalilin da yasa na kashe dan jaridar Vanguard - Wanda ake zargi Hoto: Tordue Salem
Source: Facebook

Itoro, wanda ya kasance direban motar haya ya yi bayanin cewa ya banke marigayin ne a yankin Mabushi da ke babbar birnin tarayya, Abuja, rahoton Daily Trust.

Read also

Da dumi-dumi - Direba ne ya banke dan jaridar Vanguard da ya bata, inji 'yan sanda

Ya bayyana hakan ne a lokacin da kakakin yan sandan kasar, Frank Mba ya gurfanar da shi a hedkwatar rundunar IRT, Abuja, a ranar Juma'a, 12 ga watan Nuwamba.

Da yake zantawa da manema labarai yayin gurfanar da shi, Itoro ya ce lallai ya banke wani mai tafiya a hanya da bai sani ba da misalin karfe 10:00 na daren ranar 13 ga watan Oktoba.

Sai dai, ya ce bai tsaya ya kula da mai shi ba saboda yana tsoron kada yan fashi su far masa, cewa yankin Mabushi inda hatsarin ya afku sanannen matattarar yan fashi ne, don haka ya tsorata.

Ya ce:

"Na yi zaton mutumin da na banke dan fashi ne sai washegari da na ga wani fasasshiyar waya a gilashin gaban motana. wayar bata aiki don haka sai na jefar da ita. Wajen da na bige wannan mutumin, kowa ya san cewa wajen yan ta'adda ne."

Read also

Da Duminsa: An gano gawar ɗan jaridar Nigeria, Salem, da ya ɓace

Jaridar The Nation ta kuma wallafa bidiyon wanda ake zargin a yayin da yake bayanin yadda lamarin ya faru.

An gano mai laifin ne ta hanyar bincike

Da yake gurfanar da wanda ake zargin, Mba ya fada ma manema labarai cewa an kama Clement ne sakamakon wani bincike da sashin kwararru na rundunar ta aiwatar.

Ya ce Clement wanda ke tuka wata motar Camry kirar 2004 da lamba BWR 243 BK ya tona cewa shi ya banke Salem da misalin karfe 10:00 na daren ranar 13 ga watan Oktoba, 2021, a yankin Mabushi da ke Abuja amma sai ya gudu.

Gani na karshe da aka yi wa Salem wanda ya kasance dan asalin jihar Benue, ya kasance a ranar 13 ga watan Oktoba, 2021, lamarin da ya haddasa cece-kuce a kasar.

Direba ne ya banke dan jaridar Vanguard da ya bata, inji 'yan sanda

Read also

Da Dumi: Malamin addinin musulunci da CSP na bogi na cikin mutum 14 da aka kama kan kutse gidan Mai Shari'a Odili

A baya mun kawo cewa hukumar ‘yan sanda ta bayyana cewa wani direban mota ne ya kashe dan jaridar Vanguard, Tordue Henry Salem, wanda aka tsinci gawarsa a ranar Alhamis, 11 ga watan Nuwamba.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan kasar, CP Frank Mba, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 12 ga watan Nuwamba, yayin da yake gurfanar da direban a harabar rundunar IRT da ke Guzape, Abuja.

Mba ya bayyana cewa an gano gawar Salem ne a babban asibitin Wuse.

Source: Legit.ng

Online view pixel