Da Dumi-Dumi: Miyagun yan bindiga sun kai wani mummunan hari Kaduna, sun kashe mutane

Da Dumi-Dumi: Miyagun yan bindiga sun kai wani mummunan hari Kaduna, sun kashe mutane

  • Wasu yan bindiga da ake zargin fulani makiyaya ne sun kai hari kauyuka biyu dake ƙaramar hukumar Zangon Kataf a Kaduna
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa mutum 8 sun mutu a harin, yayin da wasu da dama suka jikkata
  • Zangon Kataf na ɗaya daga cikin yankunan da hare-haren yan bindiga ya yi kamari, gwamnati na ɗaukar matakai

Kaduna - Wasu yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun hallaka mutum 8 a wani sabon hari da suka kai kauyukan karamar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa kauyukan da harin ya shafa sun haɗa da Kibori da kuma Atagjah, a karkashin yankin Aytap.

Wani shugaban yanki ya bayyana cewa wasu da ake zargin yan ta'addan Fulani ne sun farmaki Kibori da yammacin ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai harin daukar fansa, sun kashe wasu matan aure tare da kone gidaje a Taraba

Jihar Kaduna
Da Dumi-Dumi: Miyagun yan bindiga sun kai wani mummunan hari Kaduna, sun kashe mutane Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Daga zuwansu suka bude wuta kan mai uwa da wabi, inda suka kashe aƙalla mutum 5, sannan wasu da dama suka jikkata."
"Maharan sun kone gidajen mutane, kuma sun lalata kayayyakin abinci yayin harin."

Yadda suka kai hari na biyu

A cewar mutumin, ranar Talata da daddare, wasu da ake zargin makiyayan ne sun sake kai hari kauyen Atagjeh.

Ya tabbatar da cewa harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum uku, yayin da wasu da dama suka ji munanan raunuka.

"Hari a yankin Aytap ya zama ruwan dare, kusan kowane kauye dake wannan yanki an taba kai hari, yayin da rayuwa da dukiyoyin mutane suka zama ba a bakin komai ba."
"Babban abin takaicin shine masu kai waɗan nan hare-haren fulani ne muke zargi, bata garin cikin su, kuma babu wasu jami'an tsaro da zasu kare mutane daga sharrin su."

Kara karanta wannan

Hukumar ICPC ta bankado yadda aka karkatar da ayyukan mazabu sama da 300 a Jigawa da Kano

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Har yanzun kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, bai ɗaga kiran wayan da ake masa ba, domin jin ta bakin hukumarsu.

A wani labarin kuma Mutum 2 sun mutu yayin da wasu yan bindiga suka yi yunkurin sace dan majalisa a wurin bikin Aure

Ɗan majalisan yace maharan sun farmaki wurin taron bikin auren da nufin su sace shi, amma sai Allah ya ɗora shi a kansu har ya samu nasarar tsira daga sharrin su.

Ya kuma miƙa godiyarsa ga Allah bisa ba shi nasara har ya kuɓuta daga yunkurin garkuwa da shi bayan ya koma gidansa dake kauyen Uquo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel