Yobe: Jama'ar da jirgin NAF ya yi wa luguden wuta suna bukatar diyya

Yobe: Jama'ar da jirgin NAF ya yi wa luguden wuta suna bukatar diyya

  • Iyalai da 'yan uwan wadanda luguden wutan jirgin rundunar sojin sama ta ritsa da su suna bukatar diyya
  • Kamar yadda aka gano, wasu daga cikin mamatan takwas sun rasu sun bar 'ya'ya da 'yan uwa da ke karkashin kulawarsu
  • Duk da rundunar sojin saman ba ta taba bada diyya ba, iyalan na son sanin cewa ko cikin dokar aikinsu hakan ta ke

Yobe - Iyalan wadanda mummunan lamarin da ya faru a jihar Yobe da su sakamakon luguden wutan da jirgin NAF ya so yi kan 'yan ta'addan Boko Haram, sun bukaci gwamnatin tarayya da ta biya su diyya.

Sun alakanta bukatarsu da dalilin cewa, gwamnati a kowanne mataki a Najeriya ba ta cika biyan diyya ba ga jama'a da aka yi wa barna, Daily Trust ta ruwaito.

Yobe: Jama'ar da jirgin NAF ya yi wa luguden wuta suna bukatar diyya
Yobe: Jama'ar da jirgin NAF ya yi wa luguden wuta suna bukatar diyya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daga ciki mutum takwas da suka rasu, tsoffafi uku da wata mata wadanda suka bar kananan yara. Akwai yara kanana hudu da suka rasa rayukansu da kuma wasu gidaje da suka kone.

Yayin da wasu wadanda lamarin ya ritsa da su ke hanyarsu ta zuwa gona, wasu ya ritsa da su ne suna kan hanyar zuwa kasuwar mako ta Geidam.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu mazauna yankin sun yadda cewa wannan harbi da aka yi wa farar hulan bisa kuskure ne. Sun ce duk da haka lamarin Allah ya tsaro, suna bukatar a biya su diyya bayan tallafin maganin da ake basu.

Rundunar sojin saman Najeriya ta amince da cewa jirgin ta ne yayi wa jama'a ruwan wuta amma bisa kuskure.

Daily Trust ta ruwaito cewa, kamar wasu lamurra irinsu da suka faru, rundunar sojin saman ba su taba batun diyya ba duk da sun ce an kafa kwamitin bincike a kan lamarin.

Kwararru da su ka yi magana sun ce wannan ne lokacin da ya fi dacewa rundunar ta yi magana kan za ta biya diyyar wadanda suka rasu.

Idan kuma ba su biyan diyya, akwai bukatar su dinga biya kan barnar da suka yi wacce ba za a iya guje wa ba a kowanne yaki da za a yi.

Matawalle: Mun daina tattaunawa da 'yan bindiga saboda sun yaudare mu

A wani labari na daban, Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara, ya ce jiharsa ta canza shawararta kan tattaunawa da 'yan bindiga saboda yaudarar gwamnatinsa da suka yi.

A baya, Matawalle ya sanar da cewa tattaunawa ce kawai hanyar da ta dace wurin yakar lamurran 'yan bindiga a kasar nan, TheCable ta ruwaito.

Har ila yau, yayi kira ga takwarorinsa da su mayar da hankali wurin tattaunawa da 'yan bindigan domin samar da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel