Sojojin Najeriya sun hallaka yan ta'adda 31, sun damke 71, wasu 1,186 sun mika wuya

Sojojin Najeriya sun hallaka yan ta'adda 31, sun damke 71, wasu 1,186 sun mika wuya

  • Hedkwatar tsaro (HQ) ta bayyana irin ɗumbin nasarorin da sojojin Operation hadin kai suka samu cikin mako biyu
  • A cewar daraktan hulɗa da jama'a, Bernard Onyeuko, sojojin sun kashe yan ta'adda 31, sun kuma damke wasu 71
  • Wannan dai ya biyo bayan hare-haren da rundunar sojin ta kai kan yan ta'addan ta sama da ƙasa

Abuja - Hedkwatar tsaro ta ƙasa (HQ) ta bayyana cewa sojojin Operation haɗin kai sun hallaka yan ta'adda 31, kuma sun damke wasu 71.

Daily Nigerian ta rahoto cewa rahoton hedkwatar ya kara da cewa wasu yan ta'adda 1,186 sun mika wuya cikin mako biyu a Arewa maso gabas.

Muƙaddashin daraktan hulɗa da jama'a, Bernard Onyeuko, shine ya bayyana haka a wurin taron manema labarai kan nasarorin sojin daga 29 ga watan Oktoba zuwa 11 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Borno: Dan majalisa a ya bayyana yadda 'yan ISWAP suka kone gidan da ya ginawa dan uwansa

Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya sun hallaka yan ta'adda 31, sun damke 71, wasu 1,186 sun mika wuya Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Onyeuko yace daga cikin yan ta'addan da suka shiga hannu, akwai wata mace dake musu jigilar makamai yar kimanin shekara 19, Aisha Umar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakanan kuma ya ƙara da cewa akwai wata mata dake zaune a sansanin yan gudun hijira na Bama, Kaltumi Bakura, dake yiwa yan ta'addan aiki.

Wasu nasarorin da sojojin suka samu

Onyeuko ya bayyana cewa a wannan tsawon lokacin sojoji sun samu nasarar ceto mutum 97 da akai garkuwa da su, sannan sun kwato makamai 122.

A jawabinsa yace waɗan da suka mika wuya har da iyalansu da sun hada da maza 226, mata 406 da kuma kananan yara 555 duk a jihar Borno, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Ta ya sojojin suka samu wannan nasara?

Wani sashin jawabinsa, yace:

"Cikin mako biyu, sojojin sun gudanar da hare-hare ta sama da ƙasa a faɗin yankin arewa maso gabas, kuma an samu sakamako mai kyau."

Kara karanta wannan

Nasrun minallah: Dakarun Sojoji sun tarwatsa mayakan Boko Haram/ISWAP a kan hanyar Maiduguri

"Irin waɗan nan harin yana taimaka wa sosai wajen rage wa yan ta'addan ƙarfi da kuma hana su sakat, wanda ke sa suna mika wuya, domin canza halayen su."
"Daga cikin wuraren da sojoji ke luguden wuta ta sama da kasa a Borno da Yobe, sun haɗa da Rann, Dalayazara, Gwange Kura, Bam Buratai, Makintakuri, Muduvi da sauransu."

A wani labarin kuma gwamnatin tarayya tace Har yanzun fusunoni 3,906 sun yi batan dabo tun bayan hare-haren gidan gyaran hali a faɗin Najeriya

Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, shine ya faɗi haka, yace tun daga shekarar 2020 zuwa yanzun fursuna 4,369 ne suka tsere daga gidan yari.

Ministan yace akwai yan gidan gyaran hali dake karatun digirin farko, na biyu, har ma da digiri na uku a fannoni daban-daban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel