Jigawa: 'Yan Hisbah sun kama mutum 47 suna sheƙe ayansu, ciki har da mata 16, an ƙwace kwallaban giya 745

Jigawa: 'Yan Hisbah sun kama mutum 47 suna sheƙe ayansu, ciki har da mata 16, an ƙwace kwallaban giya 745

  • Hukumar Hisbah, reshen jihar Jigawa ta kama wasu mutane 47 da ake zargin su na aikata ayyuka na alfasha da rashin da’a ciki har da mata 16
  • Shugaban hukumar na jihar, Malam Ibrahim Dahiru ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata hira da ya yi da manema labarai a babban birnin jihar
  • A cewar Dahiru, an kama matan guda 16 ne bisa zargin su da karuwai bayan jami’an hukumar sun je sintiri gidajen giya da na karuwai da ke jihar

Jihar Jigawa - Hukumar Hisbah reshen jihar ta kama mutane 47 da ake zargin su na aikata rashin da’a ciki har da mata 16 kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kwamandan rundunar ta jihar, Malam Ibrahim Dahiru ne ya tabbatar da kamen ta wata hira da menama labarai su ka yi da shi jiya a Dutse, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Na sha banban da sauran yan siyasa, ni ba makaryaci bane – Mataimakin gwamnan Edo

Jigawa: 'Yan Hisbah sun kama mutum 47 suna sheƙe ayansu, ciki har da mata 16, an ƙwace kwallaban giya 745
Yan Hisbah sun kama mutum 47 suna sheƙe ayansu a Jigawa, ciki har da mata 16, an ƙwace kwallaban giya 745. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Bisa ruwayar jaridar The Nation, Dahiru ya ce a cikin wadanda aka kama har da wadanda ake zargin karuwai ne su 16.

Kuma an kama su ne bayan kai samamen da hukumar ta yi a gidajen giya, gidajen karuwai da sauran wuraren da mutanen banza ke zama.

Ya ce sun zagaye kananun hukumomi 11 da ke cikin jihar.

A cewar sa yayin samamen tsakanin ranar 13 ga watan Oktoba da 27, sun kwashe kwalaben giya 745.

Har ila yau ana zargin mazan da aka kama da kodai shan giya ko kuma neman mata da sauran miyagun ayyuka.

Dahiru ya ce gwamnatin jihar Jigawa na yaki da shan giya

Ya bayyana yadda shan giya ya kasance aiki na rashin da’a kuma gwamnatin jihar ta na yaki da hakan.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai farmaki, sun kashe mutane da dama sannan suka kona gidaje a kudadancin Kaduna

Dahiru ya shawarci mazauna jihar musamman matasa da su kiyaye yin ayyukan alfasha wadanda zasu iya lalata musu rayuwar su.

Ya kara da yaba wa mazauna jihar akan taimakon hukumar da su ke yi da ba su hadin kai don kawo karshen rashin da’a.

Kano: 'Yan Hisbah sun kama matashin da ya yi yunkurin sayar da kansa kan N20,000,000

A wani labarin daban, Rundunar ‘yan sandan musulunci ta Hisbah a jihar Kano ta kama wani matashi mai shekaru 26 da ya sa kan sa a kasuwa.

A wata tattaunawa da BBC Pidgin ta yi da kwamanda janar na rundunar, Sheikh Harun Ibn-Sina ya bayyana hakan.

Ibn-Sina ya ce sun kama matashin ne saboda abinda ya aikata ya ci karo da koyarwar addinin musulunci.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel