Kano: 'Yan Hisbah sun kama matashin da ya yi yunkurin sayar da kansa kan N20,000,000

Kano: 'Yan Hisbah sun kama matashin da ya yi yunkurin sayar da kansa kan N20,000,000

  • ‘Yan Hisbah sun yi ram da matashi mai shekaru 26 da ya sa kan sa a kasuwa
  • Kwamanda janar na rundunar, Sheik Harun Ibn-Sina ne ya bayyana wa BBC Pidgin hakan
  • A cewarsa, abinda matashin ya yi ya ci karo da koyarwar addinin Islama

Kano - Rundunar ‘yan sandan musulunci ta Hisbah a jihar Kano ta kama wani matashi mai shekaru 26 da ya sa kan sa a kasuwa.

A wata tattaunawa da BBC Pidgin ta yi da kwamanda janar na rundunar, Sheikh Harun Ibn-Sina ya bayyana hakan.

Ibn-Sina ya ce sun kama matashin ne saboda abinda ya aikata ya ci karo da koyarwar addinin musulunci.

Kano: 'Yan Hisbah sun kama matashin da ya yi yunkurin sayar da kansa kan N20,000,000
Yan Hisbah sun kama matashin da ya yi yunkurin sayar da kansa a Kano. Hoto: BBC Pidgin
Asali: Facebook

Ya ce babu wani dalili a musulunce da zai sa mutum ya sanya kan sa kasuwa.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Abba Ruma, Ministan Noma a zamanin 'YarAdu'a ya rasu a Landan

Dama Aliyu Na Idris ya yi yunkurin sayar da kan sa a N20,000,000 ne kamar yadda rahotanni su ka tabbatar.

A tattaunawar, kwamanda janar din Hisbah ya nuna rashin dacewar mutum ya aikata hakan inda ya ce musulunci bai yarda da wannan dabi’ar ba.

Kamar yadda kwamandan ya shaida wa BBC Pidgin:

“Eh, mun kama shi jiya da daddare kuma a wurin mu ya kwana sai dai ba mu zauna da shi mun tattauna ba tukunna.
“Da safen nan (Laraba) zan same shi don in ji ta bakin sa.”

Aliyu ya ce talauci ne sanadi

Aliyu wanda tela ne ya tattauna da manema labarai kafin a kama shi.

Ya shaida mu su cewa fatara ce dalilin da ya sa ya ke neman siyar da kan sa a N20,000,000.

Kara karanta wannan

Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba

Kamar yadda ya ce, iyayensa sun san halin da ya ke ciki kuma fatara ce ta tilasta sa aikata hakan. Da farko a Kaduna ya fara neman mai siyan sa, da bai samu ba ya zarce Kano.

“Wasu sun taya ni amma babu wanda ya kai N20,000,000,” a cewarsa.

Ya na so a siye shi a hakan ne don ya biya gwamnati harajin N5,000,000, ya ba iyayen sa N10,000,000 sannan ya ba wadanda su ka yi tallar sa N2,000,000 kuma ya ajiye N3,000,000 ga wanda ya siye sa saboda hidimomin yau da kullum.

Wani Nura Isah, mazaunin Kano da ya yi tsokaci ya ce bai dace Hisbah ta kama shi ba. A cewar sa mutane da dama gani su ke yi wasa Aliyu ya ke yi.

Kamar yadda ya ce:

“Kamata ya yi Hisbah ta zaunar da shi su ji da gaske ya ke ko kuma wasa maimakon kama shi da su ka yi. Don ‘yan Kano da dama gani su ke yi wasa ya ke yi.”

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel