Minista Pantami: Za a iya gane dan Najeriya a Intanet ta hanyar NIN

Minista Pantami: Za a iya gane dan Najeriya a Intanet ta hanyar NIN

  • Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami ya yi karin haske a kan manufar lambar shaidar dan kasa ta NIN
  • Pantami ya bayyana cewa da NIN, gwamnatin tarayya da hukumomin tsaron kasar za su iya gane dan Najeriya da ya shiga Intanet
  • Ya kuma bayyana cewa NIN zai zamo ginshikin tattalin arziki da tsaron kasar nan

Faris, kasar Faransa - Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami, ya ce lambar shaidar dan kasa, NIN zai zama ginshikin tsaron Najeriya.

Pantami ya yi magana ne a lokacin taron kungiyar hadin gwiwa da aka shirya a birnin Faris domin kara dankon zumunci tsakanin Najeriya da Faransa bayan annobar korona, rahoton The Cable.

Minista Pantami: Za a iya gane dan Najeriya a Intanet ta hanyar NIN
Minista Pantami: Za a iya gane dan Najeriya a Intanet ta hanyar NIN Hoto: Premium Times
Source: UGC

A ruwayar Punch, Pantami ya ce gwamnatin tarayya ta yi nufin samar da tushen tsaron kasar ne kan NIN domin tabbatar da ganin cewa an gane duk wani dan kasa da mazauna cikinta da suka shiga intanet.

Read also

Tuna baya: Yadda aka kusa halaka zababben gwamnan Anambra saura wata 8 zabe

Ya ce:

"Wasu daga cikin wadannan tsare-tsaren da suka zama ginshiki hatta ga tattalin arzikinmu shine samar da lambar dan kansa. Najeriya ta shiga sahun kasashen duniya ta hanyar wajabtawa yan kasa da mazauna cikinta amfani da lambar NIN.
"Wannan zai zama ginshikin tattalin arzikinmu sannan kuma ya zamo ginshikin tsaronmu cewa duk wanda ya hau yanar gizo, gwamnatin tarayya da hukumomin tsaronmu za su gane ko wanene shi.
"Kamar yadda yake a kundin tsarin mulkinmu na 1999 kamar yadda aka yi masa gyara sashi na 14(2)(b), cewa babban aikin gwamnati shine samar da tsaro da kare rayukan yan kasarta, saboda wannan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da hankali sosai kan haka sannan ya ke ta matsawa don ganin mun samar da ginshikin tattalin arzikinmu da na tsaronmu a kan lambar NIN domin sanin yan kasarmu da mazauna kasarmu.

Read also

Kungiyar PDP ta nemi Gwamna Wike ya nemi takarar kujerar shugaba Buhari a 2023

"Kamar yadda yake zuwa yau, rajista ya haura miliyan 67 kuma abu mafi muhimmanci mun yi nasarar daukar nau'in mutane masu muhimmanci da suka fito don yin kasuwanci."

Ya kara da cewa a yanzu NIN ya zama abun bukata domin cin moriyar ayyukan gwamnati kuma saboda haka ya kamata masu zuba jari su samu nutsuwar zuciyar yin kasuwanci a Najeriya.

Ya ba masu zuba jari tabbaci kan kokarin da gwamnati ke yi domin kara inganta tsaron Najeriya, cewa kwanan nan kasar za ta zuba na'urorin zamani domin inganta tsaronta ta intanet.

Yana da hatsari: FG ta yi gagarumin gargadi ga 'yan Najeriya kan hada katin SIM da NIN

A gefe guda, mun kawo a baya cewa hukumar sadarwa ta Najeriya ta aika da wani sako zuwa ga ‘yan Najeriya.

Hukumar ta bukaci ‘yan Najeriya da kada su yarda a hada lambarsu ta dan kasa da katin sim din wani daban, jaridar Punch ta rahoto.

Read also

Yan bindiga sun yi awon gaba da ma'aikatan gwamnatin Kaduna a Zaria, dukkansu mata

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Daraktan NCC, Efosa Idehen.

Source: Legit.ng

Online view pixel