Labari da Hotuna: Ma'aikatan Gwamnatin tarayya sun garkame babban ma'aikata, sun bukaci a tsige matar minista

Labari da Hotuna: Ma'aikatan Gwamnatin tarayya sun garkame babban ma'aikata, sun bukaci a tsige matar minista

  • Ma'aikata sun nuna fushinsu kan yadda matar minista ke tafiyar da ma'aikatar da suke aiki kuma masu ruwa da tsaki sun yi gum
  • Ma'aikatan sun garkame kofar shiga ma'aikatar kasuwanci da zuba hannun jari, sun bukaci a cire matar minista daga ofishinta
  • A cewarsu sun mika kukan su ga minista Aisha Abubakar, da shugaban ma'aikata amma har yanzun ba'a ɗauki mataki ba

Abuja - Ma'aikatan gwamnati dake aiki a ma'aikatar kasuwanci da zuba hannun jari sun barke da zanga-zanga tare da garkame babbar kofar shiga ma'aikatar ranar Laraba.

Premium Times tace yayin wannan zanga-zanga ma'aikatan sun bukaci a cire sakataren dindindin na ma'aikatar daga mukaminta.

Sakataren ma'aikatar, Evelyn Ngige, mata ce ga ministan kwadugo da samar da aikin yi, Dakta Chris Ngige.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bi gida-gida a Katsina, sun hallaka mutane tare da kone dukiyoyi

Ma'aikatan tarayya
Labari da Hotuna: Ma'ikatan Gwamnatin tarayya sun garkame babban ma'aikata, sun bukaci a tsige matar minista Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Masu zanga-zangan sun zargi matar ministan da gaza tafiyar da ma'aikata yanda ya dace da kuma nuna halin ko in kula ga walwala da jin daɗinsu.

Mutanen sun fara zanga-zangar su ne da misalin ƙarfe 9:30 na safe, inda suka saka makulli suka kulle babbar kofar shiga ma'aikatar.

Ina matsalar take?

Shugaban haɗakar ƙungiyoyin ma'aikatan, Okonkwo Onwuyai, ya bayyana cewa sakatariyan ta rike kuɗin tafiyar da ma'aikata duk da cewa gwamnati ta turo.

Onwiyai yace ƙungiyarsu ta sanar da ministan kasuwanci da zuba hannun jari, Aisha Abubakar, da shugaban ma'aikata, Folasade Yemi-Esan, su sa baki, amma babu wani mataki da aka ɗauka.

"Ƙungiyar mu ta na kira ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya cire Evelyn Ngige daga ma'aikatar baki ɗaya."

Wasu daga cikin hotunan zanga-zangar

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Dalibai sunyi barazanar tsayar da harkoki cak a Zaria saboda sace ma'aikatan kananan hukumomi 13

Ma'aikatan tarayya
Labari da Hotuna: Ma'ikatan Gwamnatin tarayya sun garkame babban ma'aikata, sun bukaci a tsige matar minista Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ma'aikatan tarayya
Labari da Hotuna: Ma'ikatan Gwamnatin tarayya sun garkame babban ma'aikata, sun bukaci a tsige matar minista Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A wani labarin kuma Rikici ya barke tsakanin Matar mamallakin ginin mai hawa 21 da yan uwansa kan kuɗi

A ranar Asabar, iyalan waɗan da dogon gini mai hawa 21 ya rufta da su, suka fara zuwa wuraren da aka ajiye gawarwaki domin duba na yan uwansu.

A wani bamgaren kuma matar Femi Osibona, wanda ke jagorantar ginin da yan uwansa suka fara rikici kan amfani da makuɗan kudin da ya bari, da kuma motocin alfarma dake cikin gidansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel