Yadda wuta ya babbake wani soja da ɗan smogul har lahira a Seme Border

Yadda wuta ya babbake wani soja da ɗan smogul har lahira a Seme Border

  • Kusa da iyakar Seme da ke Badagry, wani lamari mai firgitarwa ya auku inda wani soja da masu sumogal din fetur 2 su ka babbake har lahira
  • Kamar yadda rahotanni su ka nuna, lamarin ya auku ne a ranar Asabar inda babura 2 dauke da man fetur su ka ci karo wanda hakan ya ja tashin wuta
  • Bayan wucewar wani dan sumogal da gudu sojan ya bi shi don dakatar da shi, a hanyar su ta juyowa su koma madakatar soji su ka ci karo da wani da sumogal din wuta ta tashi

Legas - Wasu mutane 2, ciki har da soja, Saja G. Abdullahi sun babbake har lahira. Lamarin ya rutsa da Abdullahi ne inda ya yi kokarin dakatar da wani dan sumogal din man fetur da ke bisa babur a babban titin Badagry zuwa Seme.

Kara karanta wannan

Jaruma Rahama MK, matar gwamna a fim din Kwana Casa'in ta yi auren sirri

NAN ta ruwaito yadda lamarin ya auku da misalin karfe 8:15pm na ranar Asabar a wuraren Sitto inda karon babura biyu ya janyo tashin wuta.

Yadda wuta ya babake wani soja da ɗan smogul har lahira a Seme Border
Yadda wuta ya babake wani soja da ɗan smogul har lahira a Seme Border. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Rahotanni bisa rahoton Daily Nigerian sun nuna cewa Solomon Donna, wani dan sumogal din fetur ya tsere yayin da sojoji su ka tsayar da shi a matsayar su sannan wani soja ya bi shi a baya don ya kama shi.

Yadda lamarin ya auku

Rahoton ya zo kamar haka:

“Jami’an tsaron matsayar kwanar Arakab da ke Sitto a Badagy sun umarci wani mai babur da ke dauke da fetur da ya tsaya amma ya tsere.
“Hakan ya sa Abdullahi cikin hanzari ya bi shi da gudu don ya kama shi kuma ya mayar da shi madakatar sojojin.
“Sai dai yayin dawowarsu kasancewar hanya daya ce ake bi, suka ci karo da wani babur din dauke da man fetur.

Kara karanta wannan

An kuma: 'Yan bindiga sun sace wani attajirin Zamfara a karo na biyu bayan ya tsere daga hannunsu

“Sanadin haka gobara ta tashi inda Donna ya kone kurmus yayin da Abdullahi da dayan dan sumogal din su ka yi mummunar konewa.”

An samu bayanai akan yadda aka zarce da sojan da dayan mutumin zuwa babban asibitin Badagry don duba lafiyar su. Daga baya Abdullahi ya rasu a asibitin.

‘Yan uwan dan sumogal din sun tafi da gawar sa don su birne shi yayin da aka mayar da gawar Abdullahi zuwa ma’adanar gawar asibitin.

Rundunar ‘yan sandan yankin Badagry ta ce ce har yanzu ba ta samu rahoto akan lamarin ba.

'Yan sanda sun yi ram da wasu samari 2 bayan sun datse wa juna hannaye yayin kwasar dambe

A wani labarin, 'yan sanda sun yi ram da samari 2 bisa kama su dumu-dumu da laifin sare wa juna hannaye, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

An ruwaito yadda ‘yan sandan su ka kama Adamu Mohammed da Bukar Audu, bayan sun datse wa juna hannaye yayin wani fada da su ka tafka a Garin Alkali, karamar hukumar Dapchi da ke jihar Yobe.

Kara karanta wannan

'Karin bayani: Adadin wadanda suka mutu a gobarar kasuwar Abuja ya ƙaru zuwa 7

Premium Times ta bayyana yadda Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, a ranar Litinin a Damaturu ya bayyana a wata takarda.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel