Da Duminsa: 'Yan bindiga sun kashe babban soja, AVM Muhammad Maisaka tare da jikansa a Kaduna

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun kashe babban soja, AVM Muhammad Maisaka tare da jikansa a Kaduna

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna sun tabbatar da kisan tsohon sojan sama, AVM Muhammad Maisaka da wasu ‘yan bindiga su ka yi har gidan sa da ke Rigasa, karamar hukumar Igabi da ke Kaduna
  • Jami’in hulda da jama’an yankin, ASP Muhammad Jalige ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce abin ya auku ne da safiyar ranar Talata
  • Ya kara da bayyana yadda har mai gadin sa ya samu miyagun raunuka sakamakon farmakin wanda bayan kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mudassiru Abdullah ya tura jami’an sa wurin cikin gaggawa

Kaduna - Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna sun tabbatar da kisan babban sojin sama mai murabus, AVM Muhammad Maisaka, da ‘yan bindiga su ka yi a gidansa da ke Rigasa, karamar hukumar Igabi da ke jihar.

Jaridar The Nation ta ruwaito yadda jami’in hulda da jama’an rundunar na jihar, ASP Muhammad Jalige ya tabbatar wa da NAN aukuwar lamarin ranar Talata a Kaduna.

Read also

Lamari ya yi muni yayin da matasa suka ba hammata iska, suka datse hannayen juna

Da Duminsa: 'Yan bindige sun kashe babban soja, AVM Muhammad Maisaka a gidansa da ke Kaduna
'Yan bindige sun kashe babban soja, AVM Muhammad Maisaka a gidansa da ke Kaduna. Hoto: The Nation
Source: Facebook

Yadda lamarin ya faru

Jalige ya bayyana yadda lamarin ya faru da safiyar Talata, sannan har mai gadin gidansa ma ya raunana sakamakon harin.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa yan bindigan sun halaka Maisaka da jikansa wanda shima sojan sama ne mai tsaronsa wato odili sannan suka fice ba tare da sun dauki ko tsinke ba a gidan.

Ya ce bayan isar labarin wurin kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mr Mudassiru Abdullah ya umarci ‘yan sandan yankin suyi gaggawar isa wurin da lamarin ya auku.

A cewarsa:

“An kai gawar sa ma’adanar gawawwakin da ke asibiti yayin da aka zarce da mai gadin gidan sa zuwa asibiti don duba lafiyar sa.”

Ya kara da cewa za su bayyana bayanai daki-daki akan yadda lamarin ya auku nan ba da jimawa ba.

Read also

Zamfara: ‘Yan sanda sun samu nasarar ceto mutane 2 da aka yi garkuwa da su

Jalige ya bukaci mazauna Kaduna da suyi gaggawar gabatar wa jami’an tsaro bayanai masu amfani da zasu bayar da damar kama wadanda suke da alhakin yin wannan aika-aika.

'Yan bindiga sun bude wa wasu fasinjoji wuta sun halaka 3, sun kuma ƙona babura 10

A wani labarin, kun ji cewa 'yan bindiga a yammacin ranar Juma'a, sun bude wa wasu fasinjoji wuta a mahadar Umulogho a karamar hukumar Obowo ta jihar Imo inda suka kashe uku nan take, rahoton The Nation.

Harbin, da aka yi misalin karfe 7.50 na yamma, ya janyo tashin hankali a yayin da mazauna gari da masu wucewa suka cika wandunansu da iska don tsira.

A cewar wasu da abin ya faru a idonsu, sun ce maharan nan take suka tsere a cikin motarsu suka nufi Umuahia a jihar Abia yayin da suka bar mutane ukun a kwance cikin jini.

Source: Legit.ng

Online view pixel