'Yan bindiga sun bude wa wasu fasinjoji wuta sun halaka 3, sun kuma ƙona babura 10

'Yan bindiga sun bude wa wasu fasinjoji wuta sun halaka 3, sun kuma ƙona babura 10

  • Wasu miyagun mutane da ake kyautata zaton yan bindiga ne sun bindige mutum uku har lahira a jihar Imo
  • Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Imo CSP Micheal Abattam ya tabbatar da mutuwar mutanen uku
  • Har wa yau, yan bindigan kafin su tsere sun kuma biya wasu garuruwa inda suka kone baburan bayanin Allah da dama

Jihar Imo - Yan bindiga a yammacin ranar Juma'a, sun bude wa wasu fasinjoji wuta a mahadar Umulogho a karamar hukumar Obowo ta jihar Imo inda suka kashe uku nan take, rahoton The Nation.

Harbin, da aka yi misalin karfe 7.50 na yamma, ya janyo tashin hankali a yayin da mazauna gari da masu wucewa suka cika wandunansu da iska don tsira.

Kara karanta wannan

Tituna sun yi wayam babu kowa yayin da mazauna Anambra suka fara zaman gida duk da soke umurnin da IPOB ta yi

Da Dumi-Dumi: 'Yan bindiga sun yi wa mutum 3 kisar gilla a Imo
'Yan bindiga sun kashe mutum 3 a jihar Imo. Hoto: The Nation
Asali: UGC

A cewar wasu da abin ya faru a idonsu, sun ce maharan nan take suka tsere a cikin motarsu suka nufi Umuahia a jihar Abia yayin da suka bar mutane ukun a kwance cikin jini.

Yan bindigan sun kuma kona babura kimanin 10 a garin Isinweke a karamar hukumar Ihitte/Uboma da garin Oriagu a karamar hukumar Ehime Mbano a jihar ta Imo.

Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da afkuwar lamarin

Mai magana da yawun yan sandan jihar Imo, CSP Micheal Abattam ya tabbatar da afkuwar lamarin kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ya ce:

"An tabbatar, mutane uku sun rasu. Za mu bada cikakken bayani nan gaba."

A baya-bayan nan dai ana yawaita kai hare-haren yan bindiga a yankin kudu maso gabas.

Kara karanta wannan

Hotunan jama'ar Anambra suna tururuwar karbar katikan zabensu kafin Asabar

An zargin haramtaciyyar kungiyar masu neman kafa kasar Biafra wato IPOB ce ke kai hare-haren amma kungiyar sau da yawa ta musanta hakan.

Yan bindiga sun kai hari ofishin yan sanda, sun saki wadanda aka tsare sun kona motocin sintiri

A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, a ranar Litinin, sun kai hari hedkwatar yan sanda da ke karamar hukumar Ohaukwu da ke jihar Ebonyi.

A ruwayar SaharaReporters, 'yan bindigan sun kai harin ne misalin karfe 2 na dare inda suka saki dukkan wadanda ake tsare da su a ofishin yan sandan.

Maharan sun kuma kona wasu motoccin sintirin yan sanda sannan wasu jami'an yan sandan sun tsere da raunin bindiga.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel