Rashin tsaro: Buhari ya fito daga Aso Rock, ya ga abinda ke faruwa a gari, Bafarawa

Rashin tsaro: Buhari ya fito daga Aso Rock, ya ga abinda ke faruwa a gari, Bafarawa

  • Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, ya roki shugaba Muhammadu Buhari ya bar batun walwalar fadar sa ya fito ya duba arewa da halin da ta ke ciki
  • A cewar sa, ya kamata Buhari ya sa kayan jami’an tsaro ya tattaro kwamiti don kai ziyara yankin arewa maso yamma don ganin halin da ‘yan bindiga su ka sa mutane
  • Bafarawa ya bayyana halin da mutanen yankin Zamfara da Sokoto suke ciki a matsayin bala’i da tashin hankali mai tsananin yawa wanda Buhari bai taba gani ba

Sokoto - Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa ya bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya bar batun walwalar fadar sa ya kai ziyara yankin arewa maso yamma da ta’addanci ya lalata.

“Bisa tashin hankalin da muka wayi gari a kasar mu, ya kamata shugaban kasa ya fito daga fadar sa, ya sa kaki sannan ya shirya mutane ciki har da ni don su kai ziyara yankin Zamfara don ganin halin da su ke ciki”, kamar yadda Bafarawa ya shaida wa BBC Hausa a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Ana kashe mutane, Shugaba Buhari zai yi bayani gaban Allah inji Tsohon Gwamna, Bafarawa

Rashin tsaro: Buhari ya fito daga Aso Rock, ya ga abinda ke faruwa a gari, Bafarawa
Rashin tsaro: Buhari ya fito daga Aso Rock, ya ga abinda ke faruwa a gari, Bafarawa. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Bafarawa ya kwatanta halin da kudu maso yamma take ciki musamman Zamfara da wasu yankin jihar Sokoto a matsayin masifa.

Ya dauki nauyin nuna wa Buhari wuraren da ta’addanci ya lalata, pmnewsnigeria ta wallafa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kowa ya san Bafarawa da mutum mai fitowa gar da gar ya yi magana ga Buhari a kan matsalolin rashin tsaro.

“Wannan annobar rashin tsaron mu ta fado wa."

A cewar sa:

“Wadanda su ka je kuma su ka gani ne kadai za su iya bayyana halin da Zamfara da Sokoto su ke ciki.
“Kuma babban abin takaicin shi ne yadda kowa ya san cewa gwamnatin tarayya ce ya kamata ta kula da tsaron kasa."

Bidiyoyin Buhari a Masallacin Annabi, ya kwarara wa Najeriya addu'o'in zaman lafiya

A wani labari na daban, a ranar Laraba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karasa Birnin Makkah da ke kasar Saudiya domin yin Umrah.

Kara karanta wannan

Ka daina zagin Buhari ka biya albashi da fansho: 'Yan Benue sun caccaki gwamnansu

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, a wata takarda da ya fitar, ya ce Buhari da tawagarsa sun yi wa Najeriya da jama'ar ta fatan samun zaman lafiya da tsaro.

Kamar yadda Shehu ya bayyana, ya ce addu'o'in har da na fatan habakar tattalin arziki bayan annobar korona domin karuwar kasar nan da jama'ar ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel