Najeriya zata fuskanci sabuwar barazana bayan matsalar tsaro, Ministan Tsaro

Najeriya zata fuskanci sabuwar barazana bayan matsalar tsaro, Ministan Tsaro

  • Ministan tsaro, Bashir Magashi, yace akwai babban kalubalen da rashin tsaro ke shirin haifar wa Najeriya idan ba'a ɗauki mataki ba
  • Magashi yace wajibi hukumomin tsaro su tashi tsaye domin bullo da sabbin dabarun magance haka idan ta taso
  • A cewarsa karancin abinci wanda ya jawo hauhawar farashi na ɗaya daga cikin barazanar dake fuskantar Najeriya

Abuja - Ministan tsaro, Bashir Magashi, ya bayyana cewa ƙaruwar matsalar tsaro a Najeriya yana haifar da ƙarancin abinci, kuma hakan sabuwar barazana ce.

The Cable tace Ministan ya faɗi haka ne ranar Litinin a wurin bude wani taro da hukumar tsaro ta fasaha (DIA) ta shirya a Abuja.

Ministan yace hare-haren ƙungiyar Boko Haram da ISWAP, da kuma ƙalubalen yan bindiga a Arewa ya zama wata babbar barazana ga tsaron Najeriya.

Read also

Zaben Anambra 2021: Akwai sauran rina a kaba, inji dan takarar PDP, Valentine

Bashir Magashi
Najeriya zata fuskanci sabuwar barazana bayan matsalar tsaro, Ministan Tsaro Hoto: punchng.com
Source: UGC

Hakanan Magashi yace satar ɗanyen mai a kudu-kudu da kuma masu fafutukar ɓallewa a kudu-gabas, suma wata barazana ce ga Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wace barazana Najeriya zata funkanta?

Punch ta rahoto Magashi yace:

"Abin takaicin shine wannan barazana da ake fama da ita na cigaba da zama ƙalubale ba wai ga tsaron ƙasa da tattalin arziki ba kaɗai, sabuwar barzanar ƙarancin abinci"
"Matsalar abinci shine ya jawo tashin gwauron zabi na farashin kayan abinci a faɗin kasa wanda hakan ya zama wata sabuwar barazana."
"Wannan yasa ya zama wajibi hukumomin tsaro su haɗa kai wajen dakile matsalolin kuma su nemo sabbin hanyoyin gane wasu kalubale da ka iya tasowa a gaba."

Yan ta'dda nawa suka miƙa wuya?

Magashi ya ƙara da cewa nasarorin da jami'an tsaro suka samu kwanan nan yasa yan tada ƙayar baya sama da 14,000 ne suka miƙa wuya tare da aje makamansu.

Read also

Wahalar Man Fetur: Kamfanin NNPC ya yi karin haske kan yiwuwar tashin farashin man fetur

A wani labarin na daban kuma Kotu ta hana wanda ake zargi da yiwa Gwamna Ganduje batanci rubutu a Facebook

Wata kotun majistiret dake zamanta a Kano, ta hana mutumin da ake zargi da yiwa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, batanci rubutu a dandalin Facebook.

Kotun ta ɗauki wannan matakin ne a zamanta na yau Litinin, 8 ga watan Nuwamba, 2021 yayin zaman cigaba da sauraron ƙarar.

Source: Legit.ng

Online view pixel