Kotu ta hana wanda ake zargi da yiwa Gwamna Ganduje batanci rubutu a Facebook

Kotu ta hana wanda ake zargi da yiwa Gwamna Ganduje batanci rubutu a Facebook

  • Kotu ta ɗauki matakin hana, Muazu Magaji, rubutu a Facebook kan zargin bata wa gwamna Ganduje na jihar Kano suna
  • Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gurfanar da mutumin gaban kotu ne bisa zarginsa da batanci ga Ganduje
  • Rahoto ya nuna cewa ana zargin mutumin da kiran gwamna Ganduje da wasu daga cikin iyalansa Barayi

Kano - Wata kotun majistiret dake zamanta a Kano, ta hana mutumin da ake zargi da yiwa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, batanci rubutu a dandalin Facebook.

Kotun ta ɗauki wannan matakin ne a zamanta na yau Litinin, 8 ga watan Nuwamba, 2021 yayin zaman cigaba da sauraron ƙarar.

BBC Hausa ta buga a shafinta na Facebook cewa Alkalin kotun, Mai shari'a Aminu Gabari, ya kuma janye belin da ya baiwa wanda ake zargin, Muazu Magaji Danbala kiru.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke tsakanin Matar mamallakin gini mai hawa 21 da yan uwansa kan gadon kudaɗe da motocin alfarma

Zaman kotu
Kotu ta hana wanda ake zargi da yiwa Gwamna Ganduje batanci rubutu a Facebook Hoto: BBC Hausa fb fage
Asali: Facebook

Alkalin ya ɗauki matakin janye belin ne biyo bayan gaza cika sharuɗɗan da aka gindaya masa, kuma lauyansa ya nuna cewa sharuɗɗan sun yi tsauri.

Waya shigar da ƙarar mutumin kuma akan me?

Shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa dake cikin kwaryan birnin Kano, Auwalu Aramfo, shine ya kai karar mutunen biyu, Muazu Magaji Danbala da kuma Jamilu Shehu.

Honorabul Aramfo ya garzaya gaban hukumar tsaro ta farin kaya yana neman a kwatar wa gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, haƙƙinsa kan mutanen.

A cewarsa waɗan da ake zargin sun bata wa gwamna suna da kuma wasu daga cikin iyalansa a shafin sada zumunta ta hanyar kiransu da barayi, masu karkatar da kuɗaɗen al'umma.

Wane mataki kotu ta ɗauka?

Bayan sauraron ƙarar a yau Litinin, Mai shari'a Aminu Gambari, ya ɗage sauraron shari'ar har zuwa ranar 29 ga watan Nuwamba, 2021.

Kara karanta wannan

Dakarun Hisbah sun damke karuwai 44, sun kwace kwalaben Barasa 684 a Jigawa

Legit.ng Hausa ta tattaro muku wasu daga cikin ra'ayoyin jama'a kan wannan shari'a.

Sani Bala Muhammed yace:

"Wannan mataki ya yi dai-dai, domin hakan ya zama izina ga masu zagi domin kawai kana da yancin magana."

Autan Belmat yace:

"To matasa gare ku musamman yan soshiyal mediya sai asan irin maganan da za'a ke rubutawa domin gudun bacin rana."

Badamasi Rabi'u yace:

"Lalle kam zagin mutane a kafafen sada zumunta na zamani ba dai-dai bane kuma yanzu matasa dayawa sun mai dashi fagen cin mutuncin mutane. Allah ya shiryar damu Amin."

A zaman shari'ar sheikh Abduljabbar na baya-bayan nan kun ji cewa Malamin ya sake caccakar Lauyoyinsa, inda ya nemi a bashi dama ya kare kansa

A cewar shehin Malamin Lauyoyin na shi ba su da cikakkiyar kwarewa a ilimin addini, an yi taƙaddama a zaman kotun.

Ɓangaren gwamnatin Kano sun sake gabatar da shaida ta biyu, wanda ya kasance ɗalibi ga malam Abduljabbar.

Kara karanta wannan

Kano: An gurfanar da wanda ya kira Ganduje 'ɓarawon Kano' a Facebook, kotu ta bada umurnin tsare shi

Asali: Legit.ng

Online view pixel