Wahalar Man Fetur: Kamfanin NNPC ya yi karin haske kan yiwuwar tashin farashin man fetur kwanan nan

Wahalar Man Fetur: Kamfanin NNPC ya yi karin haske kan yiwuwar tashin farashin man fetur kwanan nan

  • Kamfanin NNPC ya roki yan Najeriya su daina haɗa cinkoso a gidajen man fetur saboda tsoron za'a shiga ƙarancin mai
  • A cewar NNPC akwai sama da lita biliyan 1.7bn a ma'aji kuma wani tatatten man zai cigaba da isowa Najeriya kullum kwana
  • Yan Najeriya na ganin za'a iya samun ƙarancin man fetur a faɗin ƙasa nan gaba yayin da bikin kirsimeti ke kara kusantowa

Abuja - Kamfanin man fetur na ƙasa, NNPC, ya yi kira ga yan Najeriya kada su wahalar da kansu yayin da man fetur ya yi ƙaranci a cikin ƙasa.

Rahoton Dailytrust yace kamfanin ya tabbatar wa yan Najeriya yana da sama da lita biliyan 1.7bn a ɗakin ajiya.

A wata sanarwa ɗauke da sa hannun kakakin NNPC, Garba Deen Muhammad, kamfanin man yace babu dalilin da yan Najeriya zasu rinka jin tsoron za'a samu karancin man fetur a irin waɗan nan lokutan da kuma bayan su.

Kara karanta wannan

Shugabannin APC na shirin tsayar da gwamnan Arewa takarar shugaban ƙasa a 2023

man fetur
Wahalar Man Fetur: Kamfanin NNPC ya yi karin haske kan yiwuwar tashin farashin man fetur kwanan nan Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ba za'a samu ƙarancin fetur ba - NNPC

A sanarwan NNPC yace:

"Muna shawartan yan Najeriya baki ɗaya kada su cutar da kansu wajen cunkoson siyan man fatur, kamfanin NNPC yana da sama da lita biliyan 1.7bn a ajiye."
"Kuma akwai sauran tataccen mai da zai shigo Najeriya kullum na tsawon wasu makonni da watanni masu zuwa."

Shin dagaske za'a ƙara farashin litar man fetur?

Kamfanin ya kuma kara da cewa ba shi da masaniyar cewa gwamnati na shirin ƙara farashin litar man fetur.

A cewar sanarwan NNPC tuni hukumar dake kula da kayyade farashin mai ta ƙasa (NMDPRA) ta yi magana kan haka makon da ya shuɗe.

"Saboda haka NNPC na kira ga direbobi da sauran masu amfani da fetur su cigaba da zuwa siyan mai kamar yadda suka saba, ba tare da sun haddasa cinkoso ba."

Kara karanta wannan

Mun san ranar da za'a daina sata da garkuwa da mutane a Najeriya, Shugaban hukumar leken asiri

"NNPC na shirye-shiryen haɗa hannu da masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da an rarraba man zuwa kowane ɓangare na ƙasar nan."

A wani labarin kuma Gwamnatin jihar Ogun ta damke wani mutumi da zargin ya hallaka ɗiyarsa ta cikinsa ta hanyar lakaɗa mata dukan kawo wuka

Gwamnatin ta kuma mika shi ga rundunar yan sanda domin cigaba da bincike, amma tuni ya amsa laifinsa.

Matarsa ta bayyana cewa ta haɗa kai da mijinta wajen kashe yayansu biyu saboda talauci ya musu katutu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel