Ministan Ilimi: Shekaru 120 za a dauka kafin a iya samun likitocin da za su wadaci Najeriya

Ministan Ilimi: Shekaru 120 za a dauka kafin a iya samun likitocin da za su wadaci Najeriya

  • Ministan ilimi a Najeriya ya bayyana cewa, Najeriya na da karancin likitoci, kuma shekaru za a dauka kafin cike gibin
  • A cewarsa, zai dauki Najeriya shekaru 120 kafin ta samu adadin likitocin da take bukata su wadaci kasar
  • Ya bayyana haka ne yayin taron karramawa a wata jami'ar kiwon lafiya da aka kafa a jihar Benue

Benue - Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, a karshen mako, ya ce Najeriya za ta dauki shekaru 120 kafin ta kai ga samun yawan likitocin da kasar ke bukata ko da kuwa dukkan likitocin sun ci gaba da zama a kasar, Daily Trust ta ruwaito.

Adamu ya kuma ce Jami’ar Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FUHSO) Otukpo da ke Jihar Benue za ta cike gibin da ke tattare da bukatar adadin likitoci a Najeriya.

Read also

Hukumar NYSC ta koka kan kudin abinci: N650 ga 'yan NYSC, N1000 ga fursunoni

Ministan Ilimi: Shekaru 120 za a dauka kafin a iya samun likitocin da za su wadaci Najeriya
Ministan ilimi Adamu Adamu | Hoto: thecable.ng
Source: UGC

Ya bayyana hakan ne a wajen taron karramawa na farko na jami’ar da aka gudanar a Otada a Otukpo ta jihar Benue.

Ministan ya samu wakilcin babban sakatare a ma’aikatar ilimi ta tarayya, Arc. Sunny Echono, inda ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bisa la'akari da adadin da ake samarwa, zai dauki Najeriya kimanin shekaru 120 kafin ta samu adadin likitocin da take bukata, ko da kuwa cewa duk likitocin mu suna nan a kasar."

Amma, tare da kafa FUHSO, ministan ya ce:

"Za ta yi aiki ne a matsayin kari, ta hanyar horarwa, bincike da kirkire-kirkire don samar da ingantaccen amfani kuma kiyaye albarkatun kasa, tattalin arziki da 'yan Adam."

Tun da farko, Shugaban Jami’ar Farfesa Innocent Ujah, ya ce jami’ar “mafarki ne da ya zama gaske”, ya kara da cewa FUHSO ita ce jami’ar gwamnatin tarayya ta farko a fannin kimiyyar lafiya a Najeriya.

Read also

Kotu ta daure lauya shekaru 15 bisa laifukan tafka karya a gaban kotu

Gwamna Samuel Ortom, wanda ya ce yana alfahari da cewa jami’ar ta fara aiki, ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar Benue za ta hada gwiwa da ma’aikatar lafiya ta tarayya domin tabbatar da ingancin jami’ar, Ripples Nigeria ta ruwaito.

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari ta ware biliyoyin Nairori ga likitoci, ladan dage yajin aiki

A wani labarin, jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, gwamnatin tarayya ta yabawa kungiyar likitoci mazauna Najeriya (NARD) saboda dakatar da yajin aikin da ta yi a fadin kasar wanda ya dauki tsawon kwanaki 63.

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya bayyana haka lokacin da ya karbi shugabancin kungiyar Likitocin Najeriya (NMA), wanda ya jagoranci mambobin zartarwa na NARD, a ziyarar da suka kai ofishinsa ranar Laraba a Abuja.

Ngige, wanda ya yabawa sabon shugabancin NARD wanda Dr Godiya Ishaya ke jagoranta, saboda rokon membobinta da su koma bakin aiki.

Read also

Hotunan jami'o'i 4 na farko a duniya duk a Afrika suke, mace ta kafa 1 daga ciki

Source: Legit.ng

Online view pixel