Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari ta ware biliyoyin Nairori ga likitoci, ladan dage yajin aiki

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari ta ware biliyoyin Nairori ga likitoci, ladan dage yajin aiki

  • Gwamnatin shugaba Buhari ta yaba da yadda likitoci suka hakura suka janye yajin aiki
  • Saboda haka, gwamnati ta ware wasu biliyoyi kari kan alawus da za a ba likitocin kasar
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da likitoci mazauna Najeriya suka sanar da dage yajin aiki

Abuja - Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, gwamnatin tarayya ta yabawa kungiyar likitoci mazauna Najeriya (NARD) saboda dakatar da yajin aikin da ta yi a fadin kasar wanda ya dauki tsawon kwanaki 63.

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya bayyana haka lokacin da ya karbi shugabancin kungiyar Likitocin Najeriya (NMA), wanda ya jagoranci mambobin zartarwa na NARD, a ziyarar da suka kai ofishinsa ranar Laraba a Abuja.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi alkawari Gwamnatinsa za ta kammala ayyukan da ta fara kafin ya bar mulki

Gwamnatin Buhari ta ware biliyoyin Nairori ga likitoci ladan dage yajin aiki
Kungiyar Likitoci Mazauna Najeriya | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ngige, wanda ya yabawa sabon shugabancin NARD wanda Dr Godiya Ishaya ke jagoranta, saboda rokon membobinta da su koma bakin aiki.

Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kara jimillar kudade a cikin kasafin kudin shekarar 2022 don ba da alawus na hatsari daga naira biliyan 40 zuwa naira biliyan 47 a duk shekara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce sabon yajin aikin ba zai tabarbare ba har ya kai ga matakin da ya kai ba, idan da tsohon shugaban NARD ya ba membobinsa cikakkun bayanai.

Ministan ya ce gwamnatin tarayya ba ta da matsala da kowane likita har zuwa ranar 2 ga watan Agusta, lokacin da NARD ta fara yajin aikin.

Ya ba da tabbacin cewa duk abubuwan da ake takaddama a kansu ana magance su, gami da biyan Asusun Horar da Ma’aikatan Lafiya da alawus na musamman na Korona ga wadanda aka yi watsi da su.

Kara karanta wannan

Likitoci sun yi sa'a ni ne a matsayin minista, Ministan Buhari ya koɗa kansa

Tun da farko, a cikin jawabai daban-daban, Babban Sakataren NMA, Dakta Philip Ekpe da sabon Shugaban NARD, Dr Godiya Ishaya, sun yi kira ga ministan da ya hanzarta aiwatar da cikakken Yarjejeniyar Fahimta da suka shiga da gwamnati.

Dalilin da yasa muka janye yajin aiki bayan shafe watanni biyu muna fafatawa, Likitoci

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar bayan taronta na ranar Lahadi, NARD tace ta dauki wannan matakin ne domin baiwa gwamnatin tarayya lokaci ta cika mata bukatunta.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa zata sake nazari kan lamarin bayan mako shida, wani sashin sanarwar yace:

"Bayan kula da kokarin gwamnatin tarayya da na jihohi kan dukkan abubuwan da suka jawo yajin aikin mu, an samu cigaba sosai daga FG wajen cika alkawurra.
"Kwamitin zartarwa NEC ya dauki matakin janye yajin aikin, wanda muka fara shi tun ranar 2 ga watan Augusta.
"Saboda haka, mambobin mu zasu koma bakin aiki daga ranar Laraba 6 ga watan Oktoba, da misalin karfe 8:00 na safe."

Kara karanta wannan

Matashi ya maka IGP, DG na DSS da wasu manya a kotu kan cin zarafin 'yan Shi'a

Buhari ya gindaya sharuddan biyan albashin likitoci, ya soki yajin aiki

A baya kafin su dawo daga yajin, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ba za a biya kudaden da likitoci ke bi ba har sai an gudanar da shirin tantancewa.

Ya kuma ce za a sake nazarin alawus dinsu bayan an magance 'rarrabuwa mai zurfi tsakanin matsayin likitocin da ke yajin aiki'.

Shugaban kasar ya fadi hakan ne yayin wata ganawa da jami'an kungiyar likitocin Najeriya a fadar shugaban kasa, a cewar wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama'a, Garba Shehu ya fitar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.