Da Dumi-Dumi: Sarki a Arewa ya tube rawanin sarakuna 4 saboda alaƙa da yan ta'adda

Da Dumi-Dumi: Sarki a Arewa ya tube rawanin sarakuna 4 saboda alaƙa da yan ta'adda

  • Sarkin Bauchi, Alhaji Sulaimanu Adamu, ya tube rawanin wasu sarakunan gargajiya guda huɗu a karamar hukumar Toro
  • Sarkin ya ɗauki wannan matakin ne bisa gano cewa suna baiwa baki da ake zargin yan tada kayar baya ne wurin zama
  • Tuni dai masarauta ta umarci a maye gurbinsu da mutanen kirki, waɗan da suka dace da jagorantar al'umma

Bauchi - Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Sulaimanu Adamu, ya tube rawanin dagaci huɗu a ƙaramar hukumar Toro, jihar Bauchi.

Leadership ta ruwaito cewa sarkin ya ɗauki wannan matakin ne bisa zargin suna da alaƙa da wasu masu aikata manyan laifuka a yankin da suke jagoranta.

Sarkin Bauchi, a wata sanarwa mai ɗauke da sanya hannun sakataren masarauta, Malam Shehu Muhammad, ya bayyana yankunan dagatan da lamarin ya shafa.

Sarkin Bauchi da gwamna
Da Dumi-Dumi: Sarki a Arewa ya tube rawanin sarakuna 4 saboda alaƙa da yan ta'adda Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

A cewar sanarwan yankunan da masarauta ta dakatar da sarakunan gargajiyan sun hada da, Buruku, Turkunyan Biru, Gamawa da Zomo, duk a ƙaramar hukumar Toro.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke tsakanin Matar mamallakin gini mai hawa 21 da yan uwansa kan gadon kudaɗe da motocin alfarma

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meyasa sarkin ya tsige su?

Ya kuma bayyana cewa majalisar masarauta ce ta ɗauki matakin tsige sarakunan gargajiyan bayan zargin da ake musu da baiwa baƙi da ake zargin yan tada ƙayar baya ne wurin zama a yankunan su.

Yace:

"Sarakunan gargajiyan da aka tsige suna baiwa yan tada ƙayar baya mafaka ba tare da sanar da na gaba da su ba ko hukumomin tsaro."

Sun zama barazana ga yankunan su

Hakanan kuma Sarkin Bauchi ya bayyana cewa sarakunan gargajiyan suna da hannu a lalata albarkatun daji dake Lame Bura Game Reserve kuma hakan barazanar tsaro ne ga yankunan su.

Masarautar ta umarci hakimin Lame, Alhaji Aliyu Yakubu Lame, da kuma dagacin Tama su gaggauta maye gurbin waɗan da aka tsige.

Hakanan an umarci su tabbatar da sun zaɓi mutane nagari da suka dace, sannan su miƙa sunayen su ga masarauta domin ɗaukar mataki na gaba.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa Farfesa Shehu Dalhatu na Jami'ar BUK rasuwa

A wani labarin kuma Rikici ya barke tsakanin yan Keke-Napep da jami'an yan sanda, An bindige mutum daya

Wasu na zargin cewa jami'in hukumar yan sanda ne ya daba wa direban Keke-Napep ɗin wuka yayin da wasu ke cewa bindige shi ya yi, kuma ya barshi nan kan hanya har ya mutu.

Rahotanni sun bayyana cewa rikicin dai tsakanin yan sanda da direbobin Napep ɗin ya faru ne a kan hanyar Command, Meran, Abule-Egba, ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel