Wata Sabuwa: Gwamnan APC ya rushe shugabannin kananan hukumomi 21 da kansiloli a jiharsa

Wata Sabuwa: Gwamnan APC ya rushe shugabannin kananan hukumomi 21 da kansiloli a jiharsa

  • Gwamnan Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya sallami ciyamomi 21 da kuma kansiloli dake faɗin jiharsa
  • A wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ranar Alhamis, gwamnan ya gode wa ciyamomin bisa aikin da suka yi a jihar
  • Tun a ranar 4 ga watan Fabrairun wannan shekarar da muke ciki, 2021, wa'adin mulkin zababbun ciyamomin ya ƙare

Kebbi - Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu, ranar Alhamis, ya rushe shugabannin kananan hukumomi 21 da kansiloli dake faɗin jihar Kebbi.

Wannan na ƙunashe ne a wata sabuwar sanarwa da gwamnatin jihar ta rabawa manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Gwamna Atiku Bagudu
Wata Sabuwa: Gwamnan APC ya rushe shugabannin kananan hukumomi 21 da kansiloli a jiharsa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne bayan ya karbi bakuncin ciyamomin da zasu sauka a gidan gwamnati dake Birnin Kebbi.

Kara karanta wannan

Dakarun Hisbah sun damke karuwai 44, sun kwace kwalaben Barasa 684 a Jigawa

Gwamna ya gode musu

A jawabin da ya yi lokacin ganawarsu, Gwamna Bagudu ya gode musu bisa sadaukarwan da suka yi wajen yi wa jihar Kebbi aiki na tsawon lokacin da aka zaɓe su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

"Ina godiya a gare ku, bisa aikin da kuka yi wa jiha ba tare da nuna son rai ba na tsawon wannan lokaci."

Sai dai har yanzun babu cikakken bayani daga gwamnatin jihar Kebbi, kan wa tsofaffin ciyamomin zasu miƙa wa ragamar yankunan su.

Meyasa gwamnan ya sallame su?

Legit.ng Hausa ta gano cewa wa'adin zababbun ciyamomin ya ƙare ne tun a ranar 4 ga watan Fabrairu na shekarar 2021.

Hakanan kuma hukumar zaɓe mai zaman kanta ta zaɓi ranar 5 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da zata gudanar da zaɓukan kananan hukumomi, amma kuma abin ya canza.

Kara karanta wannan

Gwamnan Legas ya kori daraktan kula da gine-gine bayan rugujewar bene mai hawa 22

A wani labarin kuma Rikici ya barke tsakanin yan Keke-Napep da jami'an yan sanda, An bindige mutum daya

Wasu na zargin cewa jami'in hukumar yan sanda ne ya daba wa direban Keke-Napep ɗin wuka yayin da wasu ke cewa bindige shi ya yi, kuma ya barshi nan kan hanya har ya mutu.

Rahotanni sun bayyana cewa rikicin dai tsakanin yan sanda da direbobin Napep ɗin ya faru ne a kan hanyar Command, Meran, Abule-Egba, ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel