'Yan ta'addan ISWAP sun sace 'ya'yan gidan sarautar Askira Uba

'Yan ta'addan ISWAP sun sace 'ya'yan gidan sarautar Askira Uba

  • Miyagun 'yan ta'addan ISWAP sun yi garkuwa da 'ya'yan gidan sarautar Askira Uba har maza uku kan hanyarsu ta zuwa Maiduguri
  • 'Yan ta'addan sun sace Mohammed Askira da kannansa biyu, wadanda dukkansu kannai ne ga mai martaba Sarkin Askira Uba
  • 'Yan ta'addan na cigaba da cin karensu babu babbaka yayin da miyagu masu kai musu bayanan sirri ke kara kaimi

Borno - 'Yan ta'addan Islamic State of West Africa Province, ISWAP, sun sace dattijo mai shekaru 50 mai suna Mohammed Askira, tare da 'yan uwansa maza biyu daga gidan sarautar Askira Uba a jihar Borno.

PRNigeria ta tattaro cewa, an yi garkuwa da su ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Maiduguri, babban birnin jihar Borno bayan halartar wani taro a garin Askira Uba.

'Yan ta'addan ISWAP sun sace 'ya'yan gidan sarautar Askira Uba
'Yan ta'addan ISWAP sun sace 'ya'yan gidan sarautar Askira Uba. Hoto daga PRNigeria.com
Asali: UGC

Majiyoyi sun sanar da cewa, dattijon mai shekaru 50 da 'yan uwansa maza biyun da aka sace duk kannai ne ga Mai Martaba Sarkin Askira Uba.

Kara karanta wannan

Yan ta'addan Boko Haram 17,000 suka mika wuya kawo yanzu, Kwamdanda Operation Hadin Kai

A yayin da 'yan ta'addan ISWAP suka tsananta garkuwa da mutane a yankin, jama'a sun dinga nuna damuwarsu kan yadda al'amuran masu kai bayanan sirri ga 'yan ta'adda ke hauhawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Suna bayyana bayanin kaiwa da kawowar jami'an tsaro da sauran mutane ga kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin, PRNigeria ta wallafa.

A cikin kwanakin nan ne kungiyar ta'addancin mai tarin hatsarin gaske ta nada Wali Sani Shuwaram, mai shekaru 45 a matsayin sabon shugaban ISWAP a yankin tafkin Chadi.

Nasara daga Allah: An bindige mai garkuwa da mutane yayin karbar kudin fansa

A wani labari na daban, rundunar hadin guiwa ta jami'an tsaro a jihar Ekiti ta halaka wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne yayin da ya je karbar kudin fansa a dajin da ke tsakanin iyakar jihohin Ekiti da Kwara.

Kara karanta wannan

An yi wata 10 babu wuta a Borno, Manyan Arewa sun yi kaca-kaca da Gwamnatin Buhari

Wata majiya ta sanar da manema labarai a Ado Ekiti cewa, jami'an tsaron da suka hada da sojoji, 'yan sanda da 'yan Bangan da Sarkin Fulanin Ekiti, Alhaji Adamu Abashe, ya kafa suka yi kisan a dajin Eruku da ke jihar Kwara, Daily Trust ta wallafa.

Jami'an tsaron sun yi kwanton bauna ne a yayin da masu garkuwa da mutanen suka bukaci a biya su kudin fansa har N2.1 miliyan bayan sace wani da suka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel