Nasara daga Allah: An bindige mai garkuwa da mutane yayin karbar kudin fansa

Nasara daga Allah: An bindige mai garkuwa da mutane yayin karbar kudin fansa

  • Jami'an tsaro hadin guiwa da suka hada da sojoji, 'yan sanda da 'yan banga sun harbe mai garkuwa da mutane yayin karbar kudin fansa
  • Lamarin ya faru ne bayan da masu garkuwa da mutane suka bukaci N2.1m kuma aka amsa za a basu, sun je daji karbar aka sakar musu ruwan wuta
  • A take 1 ya mutu yayin da aka ceci mutum 2 da aka sata inda kuma jami'an tsaro suka bi sauran miyagun da suka tsere saboda ganin jami'ai

Ekiti - Rundunar hadin guiwa ta jami'an tsaro a jihar Ekiti ta halaka wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne yayin da ya je karbar kudin fansa a dajin da ke tsakanin iyakar jihohin Ekiti da Kwara.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an yan sanda 4 a jahar Anambra

Wata majiya ta sanar da manema labarai a Ado Ekiti cewa, jami'an tsaron da suka hada da sojoji, 'yan sanda da 'yan Bangan da Sarkin Fulanin Ekiti, Alhaji Adamu Abashe, ya kafa suka yi kisan a dajin Eruku da ke jihar Kwara, Daily Trust ta wallafa.

Nasara daga Allah: An bindige mai garkuwa da mutane yayin karbar kudin fansa
Nasara daga Allah: An bindige mai garkuwa da mutane yayin karbar kudin fansa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Jami'an tsaron sun yi kwanton bauna ne a yayin da masu garkuwa da mutanen suka bukaci a biya su kudin fansa har N2.1 miliyan bayan sace wani da suka yi.

Sun je dajin domin karbar kudin fansan, amma jami'an tsaron sun boye. A take suka bindige wanda ya je karbar kudin fansan, Daily Trust ta ruwaito.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Ekiti, Sunday Abutu, ya ce an kai gawar mai garkuwa da mutanen a hedkwatarsu da ke Ado Ekiti a jiya.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun kashe wani dan bangan da suka sace bayan sun karbi kudin fansa naira miliyan biyu

Abutu ya yi bayanin cewa, "Jami'an tsaro sun ceto mutum biyu da ransu yayin da ake kokarin cafke wadanda ake zargin bayan sun tsere."

'Yan banga sun bindige mai garkuwa da mutane yayin da ya je karbar kudin fansa

A wani labari na daban, 'yan sandan jihar Adamawa sun tabbatar da sheke wani mai garkuwa da mutane da 'yan banga suka yi yayin da ya je karbar kudin fansa daga 'yan uwan wacce ya sace, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Sulaiman Nguroje, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Laraba a Yola, ya ce lamarin ya faru a ranar 26 ga watan Augusta a karamar hukumar Song ta jihar.

"Rundunar 'yan sandan jihar ta samu rahoto daga 'yan sandan Song a ranar 26 ga watan Augusta kan cewa 'yan banga sun sheke wani da ake zargi da garkuwa da mutane yayin karbar kudin fansa," Nguroje ya ce.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun musanta labarin halaka jami'an tsaro 20 da aka yi a Zamfara

Asali: Legit.ng

Online view pixel