An yi wata 10 babu wuta a Borno, Manyan Arewa sun yi kaca-kaca da Gwamnatin Buhari

An yi wata 10 babu wuta a Borno, Manyan Arewa sun yi kaca-kaca da Gwamnatin Buhari

  • A makon nan ne Dattawan Arewacin Najeriya suka yi wani zama a kan halin da kasa ta ke ciki.
  • Kungiyar manyan na NEF ta koka a kan yadda aka bar mutanen Maiduguri babu wutar lantarki.
  • NEF ta fitar da jawabin bayan zama, ta na mai kira ga gwamnati a kan lamarin tsaro da halin kasa.

Kaduna - Dattawan Arewacin Najeriya sun zargi gwamnatin tarayya da nunawa babban birnin jihar Borno, Maiduguri halin ko a kula kan batun rashin wuta.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Laraba, 3 ga watan Nuwamba, 2021, inda aka ji manyan yankin Arewa suna masu Allah wadai da gwamnatin tarayya.

Shugaban kungiyar dattawan Arewa, NEF, Farfesa Ango Abdullahi, ya fito yana kira ga gwamnati tayi duk abin da za ta iya domin kawo karshen wannan lamari.

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu ya fi zaben Anambra muhimmanci, ku sake shi don a samu zaman lafiya, Doyin Okupe

Jaridar tace tsohon shugaban jami’ar ta Ahmadu Bello da ke Zariya ya jagoranci wani zama da NEF ta yi.

A jawabin bayan taro da kungiyar ta fitar ta bakin kakakinta, Hakeem Baba-Ahmed, ta caccaki gwamnatin Muhammadu Buhari a kan tabarbarewar tsaro.

Buhari
Buhari da wasu manyan Arewa Hoto: www.thisdaylive.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jawabin da NEF ta fitar bayan taro

“Kungiya tana tare da sauran mutanen kasar nan wajen nuna fushinsu na cewa an shafe watanni 10 babu wuta a babban birnin Borno, Maiduguri.” – NEF.
“Dole duk yadda za ayi, a magance matsalar. Kuma a bi a hankali da shirin rufe duk wasu sansanin ‘yan gudun hijira ta yadda ba za a jefa wasu a matsala ba.”

Sauran batutuwan da kungiyar ta tabo

A karshen wannan taro, kungiyar NEF ta tabo batun ‘yan bindiga, tace idan an ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda zai inganta tsaro, tana goyon bayan yin hakan.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Matasan arewa sun nuna goyon bayansu ga shahararren dan siyasar kudu

Har ila yau, manyan na Arewa sun ce a bi doka wajen kawo karshen matsalolin da ake fama da su. Jaridar Opinion Nigeria ta fitar da wannan rahoto a jiya.

“Gwamnati ta duba yiwuwar samun karancin abinci nan da ‘yan watanni a yankunan Arewa saboda masifar tsadar rayuwa bayan halin da Talaka ke ciki.”

An bar mutane a duhu a Maiduguri

Tun a farkon shekarar nan kuka ji cewa Bayin Allah suna kuka a birnin Maiduguri bayan ‘Yan ta’addan Boko Haram sun datse layin da ya shigo da wuta garin

Lalata wutar lantarki da Boko Haram su ka yi, ya jawo ana zama a duhu. Har yanzu ba a yi nasarar gyara wutar ba, amma an yi alkawari kawo wata mafita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel