Miyetti Allah ga FG: Don Allah ku ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda

Miyetti Allah ga FG: Don Allah ku ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda

  • Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah Kautar Hure ta roki gwamnati ta ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'addda
  • Kungiyar ta ce 'yan bindiga basu da wani amfani, kawai suna lalata halattatun hanyoyin rayuwar 'yan Najeriya ne
  • Hakazalika, kungiyar ta yi magana kan batun shugabancin kasa a 2023, inda tace a bar zabi a hannun talakawa kawai

Bauchi - Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hure reshen jihar Bauchi ta goyi bayan kiraye-kirayen ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda a Najeriya.

Da take goyan bayan matsayar Majalisar Dattawa, Wakilai da Kakakin Majalisar da suka yi wannan kiran a baya, kungiyar ta shawarci Gwamnatin Tarayya da ta yi duk abin da ya dace don dakile barnar 'yan bindiga.

Shugabanta na jihar Bauchi, Alhaji Sadik Ibrahim Ahmad, wanda ya zanta da jaridar The Nation a ranar Lahadi 7 ga watan Nuwamba, inda ya bayyana ra'ayinsa.

Kara karanta wannan

2023: Dattijan Arewa sun yi mi'ara koma baya, sun ce za su yi aiki tare da sauran yankuna

Miyetti Allah: Don Allah ku ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda
Kungiyar Miyetti Allah Kautar Hure | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“‘Yan ta’adda mutane ne masu kokarin lalata halaltattun ayyukan al’umma, ba su da wani amfani idan da gaske gwamnatin tarayya ta ke, ya kamata ta yi abin da ake bukata tare da samar da mafita mai dorewa kan kashe-kashen da ‘yan fashi da ake kira ‘yan bindiga ke yi.”

Sai dai, a watan Satumba, Punch ta ruwaito yadda wata kungiyar Yarbawa ta O’odua Progressive Union cewa ya kamata gwamnati ta ayyana Miyetti Allah a matsayin 'yan ta'adda tare da 'yan bindiga.

Dangane da batun raba jam’iyyun siyasa gabanin zabukan 2023, ya ce a bar talakawa su zabi shugabanninsu ba tare da la’akari da kabila ba ko addini.

A cewarsa:

“Ko Bayarabe ne, Bahaushe ko Igbo, da zarar ka cancanta, ka cancanci shugabancin kasar. Batun yanki bai zama ba kuma ba zai taba zama tsarin dimokradiyya ba.

Kara karanta wannan

An yi wata 10 babu wuta a Borno, Manyan Arewa sun yi kaca-kaca da Gwamnatin Buhari

“Ya kamata mutane su nemi shugabanni masu gaskiya idan muna son hada kanmu. Shugabanninmu su ne ke haifar da matsaloli, rudani, da rikicin yanki a tsakaninmu."

Gwamnan Neja ya gano hanyar dakile 'yan bindiga, za a kakabawa makiyaya haraji

A wani labarin, Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya bayyana cewa za a dawo da tsarin karbar harajin shanu da aka fi sani da “Dogali” a jihar domin yaki da ‘yan bindiga da satar shanu a jihar, Leadership ta ruwaito.

Gwamnan jihar ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna ranar Alhamis 4 ga watan Nuwamba.

Ya ce matakin zai kuma baiwa gwamnati damar samun bayanan da ake bukata kan adadin shanu da kuma zirga-zirgarsu a cikin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel