Da dumi-dumi: Amotekun sun kama ‘yan bindiga 18 dauke da bindigogi da makamai 500 a motoci uku

Da dumi-dumi: Amotekun sun kama ‘yan bindiga 18 dauke da bindigogi da makamai 500 a motoci uku

  • Jami'an tsaron Amotekun reshen jihar Ondo, sun yi ram da wasu yan bindiga da makamai masu tarin yawa a cikin motocin bas uku
  • Babban sakataren labaran gwamnan jihar Ondo, Olabode Richard Olatunde ne ya bayyana hakan a ranar Juma'a, 5 ga watan Nuwamba
  • An tattaro cewa miyagun sun tsere shingen bincike daban-daban kafin yan Amotekun din suka damke su

Jihar Ondo - Jami'an tsaron Amotekun reshen jihar Ondo, sun kama motocin bas uku cike da 'yan bindiga 18 da kuma makamai, jaridar Punch ta rahoto.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren labaran gwamnan jihar Ondo, Olabode Richard Olatunde ya saki a ranar Juma'a, 5 ga watan Nuwamba.

Da dumi-dumi: Amotekun sun kama ‘yan bindiga 18 dauke da bindigogi da makamai 500 a motoci uku
Da dumi-dumi: Amotekun sun kama ‘yan bindiga 18 dauke da bindigogi da makamai 500 a motoci uku Hoto: Richard Olatunde
Source: Facebook

Taken sanarwar ita ce: 'Da dumi-dumi: Amotekun reshen Ondo ta kama yan bindiga dauke da bindigogi da makamai 500 a cikin motocin bas uku.'

Read also

Tituna sun yi wayam babu kowa yayin da mazauna Anambra suka fara zaman gida duk da soke umurnin da IPOB ta yi

Sanarwar ta zo kamar haka:

"Jami'an tsaron Amotekun a jihar Ondo sun kama wata motar bas cike da makamai 500 a karkashin kujerun motar.
"Hakazalika sun kama makamai daban-daban da suka kama da wukake da bindigogi shirye a jakunkunan fata.
"An kama mutane 18 da ake zaton yan bindiga ne tare da motar yayin da bas biyu suka tsere.
"Da yake gurfanar da masu laifin a gaban manema labarai a Akure, kwamandan Amotekun na jihar, Adetunji Adeleye, ya ce motocin bas din uku sun tsere daga shingen bincike daban-daban kafin aka kama su a garin Ondo."

A halin da ake ciki, Gwamna Rotimi Akeredolu ya yaba ma jami'an na Amotekun kan cike gibin da jami'an soji suka bari a jihar, Sahara Reporters ta ruwaito.

Read also

Rashin tsaro: Gwamnatin Zamfara ta hukunta mutane sama da 1, 000 da suka saba doka

Jami'an soji sun bar shingen bincike a jihar bisa zargin rashin biyansu alawus da gwamnatin jihar bata yi ba.

A wani labarin, rundunar yan sanda a jihar Borno, ta yi watsi da rahoton cewa 'yan ta'adda sun yi garkuwa da jami'anta biyu a wani hari da aka kai karamar hukumar Magumeri a ranar Laraba.

Kwamishinan yan sandan jihar, CP Abdu Umar, ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Maiduguri cewa harin bai shafi yan sanda ba, rahoton The Guardian.

A ruwayar Daily Nigerian, Umar ya yi bayanin cewa 'yan ta'addan da ake zaton yan ISWAP ne sun kuma cinna wuta a wani karfen sabis na waya sannan suka sace janareto.

Source: Legit.ng

Online view pixel