Rundunar yan sanda ta karyata batun sace jami’anta a harin da ISWAP ta kai Borno

Rundunar yan sanda ta karyata batun sace jami’anta a harin da ISWAP ta kai Borno

  • Rundunar yan sandan jihar Borno ta karyata batun sace jami’anta a wani hari da yan ta'addan ISWAP suka kai yankin Magumeri
  • Kwamishinan yan sandan jihar, CP Abdu Umar, ya ce harin da mayakan suka kai bai shafi ofishin yan sanda ba kamar yadda ake ta yayatawa
  • A ranar Laraba da ta gabata ne mayakan kungiyar ta'addancin suka kai farmaki wani asibiti a yankin na Magumeri

Magumeri, Jihar Borno - Rundunar yan sanda a jihar Borno, ta yi watsi da rahoton cewa 'yan ta'adda sun yi garkuwa da jami'anta biyu a wani hari da aka kai karamar hukumar Magumeri a ranar Laraba.

Kwamishinan yan sandan jihar, CP Abdu Umar, ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Maiduguri cewa harin bai shafi yan sanda ba, rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Miyagun yan bindiga sun bi tsakar dare sun yi awon gaba da mata zalla a Neja

Rundunar yan sanda ta karyata batun sace jami’anta a Borno
Rundunar yan sanda ta karyata batun sace jami’anta a Borno Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A jawabin nasa da yayi a yau Juma'a, 5 ga watan Nuwamba, CP Umar ya ce:

"Labarin da ke yawo cewa an kai farmaki ofishin yan sanda a Magumeri, tare da yin sace-sace da kona shi da kuma batun yin garkuwa da jami'ai biyu ba gaskiya bane.
"Ba a kai hari ofishin yan sandan ba kuma ba a yi garkuwa da kowani jami'in dan sanda ba sannan ba a saki wadanda aka tsare ba kamar yadda aka yi ikirari.
"Yan ta'addan basu saci magunguna ba, amma sun tafi da zanuwan gado, tawul da kujeru a wani karamin asibiti da ba a amfani da shi. Sun kuma sanya wuta a ciyawar da ke kewaye wanda bai shafi ginin ba."

A ruwayar Daily Nigerian, Umar ya yi bayanin cewa 'yan ta'addan da ake zaton yan ISWAP ne sun kuma cinna wuta a wani karfen sabis na waya sannan suka sace janareto.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an yan sanda 4 a jahar Anambra

ISWAP sun farmaki asibiti, sun bankawa karfen sabis wuta a Borno

A baya Legit Hausa ta kawo cewa wasu da ake zaton mayakan ISWAP ne sun kai hari wani asibiti sannan suka kona karfen sabis a yankin karamar hukumar Magumeri da ke jihar Borno. Lamarin ya afku ne a yau Laraba, 3 ga watan Nuwamba.

Wani shaida ya ce bayan sun kai farmaki hedkwatar karamar hukumar, sai suka fara harbi ta kowani sako.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa maharan sun sace wasu magunguna da sauran kayan asibiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel