Da dumi-dumi: ISWAP sun farmaki asibiti, sun bankawa karfen sabis wuta a Borno

Da dumi-dumi: ISWAP sun farmaki asibiti, sun bankawa karfen sabis wuta a Borno

  • Mayakan ISWAP sun kai farmaki a karamar hukumar Magumeri da ke jihar Borno
  • Maharan sun kona karfen sabis sannan suka kai hari asibiti tare da sace magunguna da wasu kaya
  • Majiya ta kawo cewa maharan sun fafata da sojoji a harin wanda ya faru a ranar Laraba, 3 ga watan Nuwamba

Magumeri, jihar Borno - Wasu da ake zaton mayakan ISWAP ne sun kai hari wani asibiti sannan suka kona karfen sabis a yankin karamar hukumar Magumeri da ke jihar Borno.

Lamarin ya afku ne a yau Laraba, 3 ga watan Nuwamba.

Da dumi-dumi: ISWAP sun farmaki asibiti, sun bankawa karfen sabis wuta a Borno
Da dumi-dumi: ISWAP sun farmaki asibiti, sun bankawa karfen sabis wuta a Borno Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Wani shaida ya ce bayan sun kai farmaki hedkwatar karamar hukumar, sai suka fara harbi ta kowani sako.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa maharan sun sace wasu magunguna da sauran kayan asibiti.

Kara karanta wannan

Dakarun Hisbah sun damke karuwai 44, sun kwace kwalaben Barasa 684 a Jigawa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiya ta tsaro ta bayyana cewa yan ta’addan sun raba kansu gida biyu ne.

Majiyar ta ce yayin da sojoji ke musayar wuta da bangare guda, sai daya bangaren suka shiga asibitin don sace magunguna, sirinji da wasu zannuwan gado.

Majiyar ta ce:

“Sun kai farmaki garin ta baya, inda suka kona karfen sabis din Airtel sannan suka kakkabe asibitin.
“Sun tafi da magunguna, sirinji da wasu zanuwan gado.”

Magumeri yana kimanin kilomita 40 daga Maiduguri, babbar birnin jihar.

Aƙalla Dakarun yan sanda 2 da soja ne suka mutu yayin musayar wuta da mayaƙam ISWAP a Borno

A gefe guda, mun ji cewa akalla jami'an yan sanda biyu da soja ɗaya aka kashe yayin wata gwabzawa da mayakan ISWAP a Malamfatori, jihar Borno.

A ranar Laraba da muke cike da yamma, yan ta'adda da ake zargin mayaƙan ISWAP ne suka yi kokarin kutsa kai don tilas su shiga garin.

Kara karanta wannan

Kaduna: Duk da datse layikan sadarwa, 'yan bindiga sun sace mutum 9, sun bukaci N50m

Wata majiya daga cikin jami'an tsaron, yace:

"Yayin wata musayar wuta da muka yi yau a garin Malamfatori, mun rasa jami'an tsaro uku, yan sanda biyu da kuma soja ɗaya."

Asali: Legit.ng

Online view pixel