Hoton karshe na ginin da ya rubto a Legas: Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da wannan gini

Hoton karshe na ginin da ya rubto a Legas: Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da wannan gini

Labari maras dadi ya bayyana ranar Litinin cewa wani dogon gini ya ruguje a garin Ikoyi, jihar Legas, a kudu maso yammacin Najeriya.

Rahotanni sun tabbatar mana cewa wannan zungureren gini da yake yankin Alexandria Avenue a unguwar ta Ikoyi ya na da tsawon hawa 21.

Shugaban hukumar LASEMA, Dr. Femi Oke-Osanyintolu yace ba zai iya cewa mutane suna cikin ginin a lokacin da abin ya faru ba, ko kuma wannan ginin kango ne a halin yanzu.

Adadin mutanen da suka rasu sakamakon rushewar gini a unguwar Ikoyi, jihar Legas a ranar Litinin ya tashi daga 22 ya kai 36.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa daga cikin 36 da suka rasu kawo yanzu, uku daga cikinsu mata ne sai kuma maza 33.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Mamallakin dogon gini mai hawa 21 da ya rushe a Legas ya mutu

Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da wannan gini
Hoton karshe na ginin da ya rubto a Legas: Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da wannan gini Hoto: Silvernet Reporters
Asali: Facebook

Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da ginin da ya rubto kan mutane a Ikoyo, jihar Legas kamar yaddar Silvernet Reporters ta tattaro:

1. Ginin bene 21 ne kuma an kusa kammalawa

2. Kowani daki 4 bedroom flat ne kuma ana sayarwa a farashin $1.2M

3. Dakin PentHouse kuwa $5m.

4. Abubuwan dake cikin ginin sun hada da dakin motsa jiki, rafin zamani (Swimming pool), wajen shakatawa, da talabijin na jama'a)

5. Ginin na gab da kammaluwa (80%)

6. An shirya kammalawa a 2022

7. An siyar da kashi 65% na ginin tuni

8. Asalin tsarin da gwamnati ta bada ayi ginin tsauni 15 ne, amma aka kara 6 sabanin sharadi

Mamallakin dogon gini mai hawa 21 da ya rushe a Legas ya mutu

Kara karanta wannan

Buhari ya yi tafiya, Osinbajo ya jagoranci FEC, an amince a kashe N47bn a kan wasu ayyuka

Shugaban kamfanin Fourscore Homes Limited, mai suna, Femi Osibona, ya rigamu gidan gaskiya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Osibona shine mamallakin kamfanin da yake gina dogon gini mai hawa 21, wanda ya kife a Ikoyi, jihar Lagos ranar Litinin.

Ma'aikatan dake aikin ceto a wurin, sun shaida wa jaridar cewa mintuna kaɗan da suka shuɗe aka gano gawar mutumin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel