Hukuma: Hawa 15 muka amince ya gina, amma ya wuce makadi da rawa

Hukuma: Hawa 15 muka amince ya gina, amma ya wuce makadi da rawa

  • Manajan hukumar kula da gine-ginen jihar Legas ta LASBCA, Gbolahan Oki ya sanar da yadda su ka yarje wa mai banen da ya rufta a Ikoyi gina hawa 15 amma ya gina hawa 21
  • Oki ya ce yanzu haka ya na hannun hukuma kuma zai fuskanci hukunci daidai da abinda ya aikata sakamakon asarar rayukan da aka yi ta dalilin sa
  • Ya kara da bayyana yadda mutumin ya yi amfani da kayan aiki marasa nagarta kuma ma su arha, inda ya ce a kalla mutane 50 ne ake zargin sun cutu sakamakon fadin benen

Legas - Babban manajan hukumar kula da gine-ginen jihar Legas ta LASBCA, Gbolahan Oki ya bayyana gaskiyar lamari dangane da ruftawar bene mai hawa 21 na jihar Legas.

Daily Trust ta ruwaito yadda ya ce hukumar su ta amince da gina hawa 15 ne, amma mai benen ya toshe kunnuwan sa ya gina hawa 21.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: Sarkin Birnin Gwari ya bayyana alherin da katse hanyoyin sadarwa ya jawo

Hukuma: Hawa 15 muka amince ya gina, amma ya wuce makadi da rawa
Hukuma: Hawa 15 muka amince ya gina, amma ya wuce makadi da rawa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A wata hira da wakilin NAN ya yi da Oki ta wayar salula, ya shaida masa cewa yanzu haka mai benen ya na hannun hukuma, Daily Trust ta wallafa.

Ya kara da bayyana cewa wajibi ne ya fuskanci hukunci daidai da abinda ya aikata saboda asarar rayukan da aka yi sanadin hatsarin.

Oki ya shaida cewa:

“Mai benen ya nemi izinin gina hawa 15 ne amma sai ya wuce ka’ida. Yanzu haka mun gano cewa abubuwan da ya yi amfani da su wurin yin aikin benen masu arha ne kuma marasa nagarta.”
“Abubuwan da ya yi amfani da su wurin ginin ba su da kyau. Kuma ya nemi izinin gina hawa 15 amma ya bige da gina hawa 21.”
“Ina ganin yanzu haka yana hannun hukuma, don tuntuni aka kama shi.”

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Kwankwaso ya bayyana ra'ayinsa kan tafiya da Shekaru a siyasa

Yanzu dai mutane 3 ne su ka rasu amma ana ci gaba da bincike

GM ya ce an samu nasarar ceto mutane 4 masu rai yayin da 3 suka riga mu gidan gaskiya, kuma yanzu haka ana ci gaba da kara kokarin ceto wasu.

Ya kara da bayyana yadda injina 4 su ke kan aikin binciko jama’a don gano ko akwai sauran masu rai ko gawawwaki.

An samu rahoto a kan yadda mutane a kalla 50 ne su ka cutu sakamakon rushewar ginin.

Ginin shi ne mai lamba ta 20 a layin Gerrard, kuma ya fadi ne da misalin karfe 3pm a ranar Litinin.

Dinbin mutane sun makale carko-carko yayin da gini mai hawa 20 ya ruguje a Najeriya

A wani labari na daban, Labari maras dadi yana zuwa mana cewa wani dogon gini ya ruguje a garin Ikoyi, jihar Legas, a kudu maso yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsoro da zaman dardar: Yadda shirin NYSC ya zama abin tsaro ga 'yan bautar kasa

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 1 ga watan Nuwamba, 2021, cewa wannan dogon gini da ke unguwar Ikoyi ya kife dazu da rana.

Rahotanni sun tabbatar mana cewa wannan zungureren gini da yake yankin Alexandria Avenue a unguwar ta Ikoyi ya na da tsawon hawa 20.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel