Mangal zai bi sahun Dangote da BUA, zai gina sabon kamfanin Siminti a Najeriya

Mangal zai bi sahun Dangote da BUA, zai gina sabon kamfanin Siminti a Najeriya

  • Mammalakin kamfanin jirgin zaman MaxAir zai gina sabon masana'antar hada Siminti a Najeriya
  • Mangal ya bayyana cewa wannan sabuwar masana'antar za tayi amfani da fasahar zamani a wannan masana'antar
  • Za'a kwashe shekaru uku ana gina wannan masana'anta kuma za ta ci biliyoyin nairori

Kamfanin Mangal da wani kamfanin kasar Sin, Sinoma, sun yi yarjejeniya na ginin masana'antar Siminti ton milyan uku da kuma tsiron makamashin 50- megawatt a jihar Kogi.

Shugaban kamfanin Mangal, Engr. Fahad Mangal, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Alhamis.

Jawabin yace za'a kammala ginin masana'antar a 2024 kuma za'a zuba $600 million wajen ginin.

Jawabin yace:

"Wannan Masana'antar zai yi amfani da fasaha ta zamani wajen hada Siminti kuma ba tare da bata yanayi ba."

Kara karanta wannan

Wannan auren zai yi zafi: Amarya tayi banza da Angonta wajen Walimar Aure

"Mangal na zuba jarinsa a sashen Siminti a yammacin Afrika domin taimakawa tattalin arzikin Najeriya wajen gine-ginen manyan ayyyuka da gidaje."

Mangal zai bi sahun Dangote da BUA
Mangal zai bi sahun Dangote da BUA, zai gina sabon kamfanin Siminti a Najeriya Hoto: Hajj
Asali: Facebook

Bidiyon hamshakan yan kasuwa sanye da kayan harami cikin jirgi ya bayyana

A wani labarin kuwa, attajirin nahiyar Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cikin bidiyo tare da attajirai irinsa cikin jirgin sama.

A cikin faifan bidiyon an ga Aliko Dangote tare da wasu cikin jirgin sanya da kayan Ibadah na Umrah da suka gudanar a Makkah.

Daga cikin wadanda ke cikin jirgin akwai shugaban kamfanin BUA, Alhaji Abdul Samad Isyaka Rabiu, da kuma Shugaban kamfanin jirgin MaxAir, Alhaji Dahiru Mangal, dss.

Yan Najeriya da dama sun bayyana cewa wannan haduwa ake nufi da Naira na gugan Naira.

Kara karanta wannan

Da dumi: An samu kwayar maganin cutar Korona, za'a fara amfani shi a kasar Birtaniya

Asali: Legit.ng

Online view pixel